Amitabh Bachchan ya bayyana alhininsa game da mutuwar shahararren jarumin fina-finan India wato Bollywwod, Shashi Kapoor a shafinsa na intanet, inda ya ce '' ina za mu kai wannan rayuwa?
Shashi Kapoor dai ya rasu ne a ranar Litinin, 4/12/2017 da yamma a asibitin Kokilaben da ke Mumbai.
Shashi Kapoor wanda ya yi farin jini a wajen miliyoyin ma'abota kallon fina-finan India, ya yi fama da cutar koda ne.
Amitabh Bachchan, wanda suka fito a fina-finai 16 da Shashi Kapoor, abokinsa ne na kut da kut.
Wata dangantaka ma tsakaninsu ita ce, 'yar Amitan wato Shweta ta auri wani dangin su Shashi Kapoor.
Amitabh Bachchan, ya yi matukar kaduwa da ya samu labarin rasuwar Shashi Kapoor, inda har ya yi wani rubutu a shafinsa na intanet game da abubuwan da zai iya tunawa a tsakaninsu.
Amitabh ya shaida wa Rumi Jafri, wani marubuci a India irin halayen Shashi Kapoor da ya yi koyi da su suka kuma matukar taimaka masa a rayuwarsa.
Daga ciki akwai:
Me ya sa Shashi Kapoor ya kira Tasi?
Shashi Kapoor ya kanyi tafiya da sanda ko kwagiri
Hoton da ke kasa ya kunshi Shashi Kapoor da Raj Kapoor da kuma Shammi Kapoor.
Amitabh ya ce,' a Lokacin a zuciyata ina son na zama jarumi, to amma ko da na ga wannan hoto sai na karaya ganin irin wadannan shahararrun jarumai na fitowa a cikin fim.
A wuraren shekarar 1969, na yi kokari na shiga harkar fina-finai, a lokacin na bukaci wasu abokan Shashi Kapoor su gabatar da ni a wajensa.
Ko da na bayyana musu bukatata, sai suka ce ai ba shi da matsala domin shi mutum ne mai faran-faran don haka ba shi da wuyar sabo.
A haka aka kai ni wajensa muka hadu, fuskarsa cike da fara'a ya kuma karbe ni hannu bibbiyu.
Wasu daga cikin halayyar Shashi Kapoor
Amitabh Bachchan ya ce 'Idan yana magana, za a ji alamun keta a muryarsa, sannan kuma muryarsa mai sanyi ce wadda idan ya yi magana za ka fahimci abinci da yake nufi cikin sauki'.
Kazalika halayyarsa wajen gabatar da kansa, abin sha'awa ce.
Wannan halayyar tasa ta taimaka kwarai da gaske wajen gane mutane, musamman idan mutum na zuwa wajen ka akai-akai ka kuma manta sunansa, domin da zarar Shashi Kapoor ya gabatar maka kansa, to kai ma nan da nan za ka gabatar masa da sunanka.
A gaskiya na karu matuka da irin wannan halayya ta Shashi Kapoor in ji Amitabh Bachchan.
Amitabh ya ce, ''yanayin gyaran gashin Shashi Kapoor ma na burgeni, domin a kanannade yake, ga tsayi kuma, amma duk da haka bai rufe masa fuskarsa ba.''
Ya ce, 'Nakan yi sha'awar gyaran gashin har ma na ce dama haka nawa yake'.
Mr Bachchan ya ce, Shashi Kapoor ya jima yana fama da jinya, kuma tun bayan rasuwar matarsa Jennifer, sai ya daina kula da kansa.
Ya ce, 'A lokuta da dama idan an kwantar da ni a asibiti, shi ma yana asibitin, nakan je na duba shi, amma daga bisani sai na daina zuwa na duba shi, ba haka kawai na daina zuwa duba shi ba, saboda idan ya kwanta a asibiti, bana son na je ne naga kyakkyawan abokina a wani hali marar kyan gani'.
Shashi Kapoor abokina ne sosai, don yakan kira ni da suna Babua, in ji Amitabh.
Amitabh ya ce, zan jima mutuwarsa na raina, ya bar gurbin da zai yi wuyar cikewa.
Source: BBC Hausa