Ma'aikatan sa-kai na agaji a Syria sun kwashe kashin farko na yaran da ke cikin wani mummunan hali na rashin lafiya daga yankin da 'yan tawaye ke iko da shi a kusa da Damascus.
Kungiyoyin bayar da agaji sun bukaci Shugaba Assad da ya bayar da dama a samu a shiga a yi wa tarin yaran da ke cikin matukar bakutar taimako, ciki har da wasu yara bakwai da ke fama da cutar daji.
Yanayin lafiyar da mazauna yankin gabashin Ghouta ya shiga wani mataki na kaka-ni-kayi ne bayan shekara hudu da yankin yake rike a hannun mayaka masu tayar da kayar baya.
An ga yara da dama sanye da tufafin da ke musu maganin tsananin sanyin da ke addabarsu, iyayensu mata na sanya su cikin motocin daukar marassa lafiya ana tafiya da su asibitoci a Damascus.
Yaran marassa lafiya na daga tarin wadanda ke cikin mawuyacin hali wadanda aka mika jerin sunayensu ga majalisar dinkin duniya tun wata biyu da ya gabata.
Mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross a Geneva, Anastasia Isyuk ta ce, tana fatan za su samu damar ci gaba da wannan aiki na kwashe yaran marassa lafiya, tare da fatan bangarorin biyu da ke yaki za su taimaka wa aikin.
Kuma ana matukar maraba da duk wani aiki na bayar da agaji.
Takwarar kungiyar agajin ta Red Cross, wato Red Cresent ta ki bayar da bayanin yadda aka cimma wannan yarjejeniya ta kwasar yaran, illa dai ta ce an cimma matsaya ne bayan doguwar tattaunawa da hukumomin Syria.
'yan wasu kalilan din likitoci ne kawai suke aikin kula da lafiyar mutane kusan dubu 400 a yankin na Gabashin Ghouta.
Yankin dai na daga cikin wadanda aka lasafta na wadanda aka daina bude wuta a cikinsa, amma kuma rahotanni na cewa dakarun gwamnatin Syria na ci gaba da ruwan bama-bamai a cikinsa a 'yan makonnin nan.
Yayin da ake cikin wannan yanayi, ita kuwa Rasha ta ce an kawo karshen babbar fafatawar da ake yi a Syrian ta neman murkushe kungiyar IS ta masu ikirarin jihadi.
Sai dai ta ce muhimmin abin da aka sanya a gaba yanzu shi ne na ganin an kawar da kungiyar Nusra Front wadda ke da alaka da al-Qaeda.
Ministan harkokin waje na Rashar Sergei Lavrov, ya ce wasu daga cikin mayakan 'yan tawaye da suka tsere daga filin daga, suna kokarin kara haduwa a cikin Syria ko kuma suna neman tserewa daga kasar.
A wasu kalaman na daban babban hafsan hafsoshin Rasha Janar Valery Gerasimov, ya yi zargin cewa Amurka na horar da tsoffin mayakan kungiyar IS a Syria a sansanin soji na Tanf wanda ke kan iyakar Syria da Iraq.
Sai dai wannan zargi ne da daman Amurka ta sha musawa tana cewa ita har yanzu tana goyon bayan kawar da kungiyar IS.
Source:BBC Hausa
Title :
Aikin Agaji Yafara Kaiwa Ga Yara A Syria
Description : Ma'aikatan sa-kai na agaji a Syria sun kwashe kashin farko na yaran da ke cikin wani mummunan hali na rashin lafiya daga yankin da '...
Rating :
5