Ba kasafai aka faye samun mace musamman musulma ba da ta yi nisa sosai a bangaren kimiyya.
Sai dai Hayat Al-Sindi, wadda 'yar asali kuma haifaffiyar kasar Saudiyya ce, ta ciri tuta a wannan fanni.
Hayat Al-Sindi ta kuma kasance mai bai wa shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmai, Islamic Development Bank, IDB, shawara kan kimiyya da fasaha.
A hirarta da Halima Umar Saleh, ta shaida mata cewa ta taso da son kimiyya ne tun tana karama, kuma ba ta taba cin karo da wani abu da ya saba da addininta ba a wannan bangare.
Kazalika ta fadi irin hobbasar da bankin ke yi don tallafawa mata a kasashen musulmai.
Ga dai yadda hirar tasu ta kasance:
Tambaya: Me ya ja hankalinki wajen zama gogaggiya a fannin kimiyya tun farko?
Amsa: Wannan tambaya ce mai kyau. Abun ya faro ne a lokacin da nake da shekara biyar. Kimiyya na matukar ban sha'awa.
Ina tuna lokacin da nake da wani dan karamin kati da nake wasa da shi, wanda ake iya duba yanayin dare da sararin samaniya. To wannan ya kan sani tunanin duniyar da samaniya da abun da zai faru nan gaba.
Kuma na yi sa'a ina da mahaifin da ke koya min duk abun da nake so. Don haka ya taimaka min kwarai wajen bani labaran masanan da suka yi wa al'umma wani abu na bajinta ta bangaren lafiya da adabi da kuma ilimin kimiyyar Physics.
Kuma ina karanta littatafan manyan masana kimiyya da ma na malaman musulunci irinsu Ibn Sina da Jabir bn Hayyan. Kuma gaskiya ni su ne gwarazana.
Tambaya: Wasu lokutan idan mutum musamman musulmi ya yi nisa a fannin kimiyya, ya kan ci karo da wasu batutuwa masu sarkakiya da suka yi hannun riga da addininsa, kuma za su iya saka masa shakku. Ganin cewa ke musulma ce da ta fito daga cibiyar musulunci wato Saudiyya, ko kin taba cin karo da wani abu a kimiyya da ya saba da addininki?
A gaskiya a lokacin da na bar kasata don zuwa Ingila don karantar kimiyya, ina jin duk duniya ta yi amanna cewa kimiyya ta yi hannun riga addini, sai dai ba haka abun yake ba a musulunce, saboda a musulunci ayoyin Al-kur'ani da dama da hadisan Manzon Allah SAW, sun ba mu kwarin gwiwa mu kirkiri wani abu, mu yi bincike a kansa, mu yi sharhi, mu kuma yi tambaya a kansa.
Amma a kasashen yamma suna ganin kamar kimiyya ta yi hannun riga ne da addini.
To ni a ganina idan muna kimiyya ba wai za mu yi bincike kan wanene ya samar da wani abu ba, kamata ya yi mu yi bincike kan dalilin da ya sa aka samar da abun, ta haka ne za mu kasance cikin wadanda suka yi nasarar gano wani abu, ba wai batun waye ya yi halitta ba, Allah ne ko kuwa komai samuwa ya yi haka nan.
Idan mutane ba su gane ba, ya kamata mutum ya yi musu bayani cewa idan mutum yana da addini hakan ba zai hana shi kirkiro abubuwa ba, kamar misali Elbert Einstein,Bayahude ne amma kuma masanin kimiyya.
Don haka ni dai a bangarena, addinina da al'adata ba su hanani yin binciken kimiyya ba.
Kuma a al'adar kasashen yamman ma ba wai suna nufin idan kana da addini shi kenan kuma ba za ka shiga cikin al'amuran kimiyya ba.
Babban abun da ake bukata shi ne ka gano mece ce kimiyya, ka yi binciken me ya sa aka samar da abu kaza ta hanyar da abun yake. Don haka ina ganin za ka ilimintar da mutane ne idan ka yi binciken da ya kamata.
Wasu mutanen sun sha gaya min cewa ba zan iya kimiyya ba saboda yadda nake rufe jikina suna ganin kamar ba zan sake ba wajen yin bincike, amma ni na san a addinina da al'adata ba haka ba ne, abun da nake bukata shi ne na yi bincike, na yi tambayoyi don gano abun da nake son ganowa.
Tambaya: Bari mu dawo kan batunwajen aikinki na bankin IDB, wanne irin kalubale mata ke fuskanta a kasashen Musulmai,kuma wane taimako bankin IDB ke ba su?
Amsa: Wannan tambaya ce mai kyau. A gaskiya mata kan fuskanci matsaloli a ko wanne yanki na duniya, sai dai matsalolin sun sha bambam daga yanayin al'adun ko wacce kasa.
Muna da mata da suke aiki kuma suna fuskantar matsaloli har ta bangaren kimiyya da fasaha ma kamar a Amurka da Turai da Afirka da Gabas Ta Tsakiya.
Kuma muna kokarin magance matsalolin da mata ke fuskanta ne a kasashen Musulmai ta hanyar shigo da mata cikin al'umma ta hanyar ba su abubuwan da suke bukata da kuma ba su damar da ta dace.
Idan ki ka duba, mata sun fi maza tagomashi a fannin kimiyya da fasaha ba wai don ina nufin maza ba su iya ba. Kuma ko da mun tallafawa al'umma to muna kuma tallafawa mata daban.
Kuma a yanzu muna da wani sabon shiri a IDB ta yadda za mu karfafawa mata su zama injiniyoyi masu nazarin hasken rana, da kuma tallafa musu da kayan aikin da suke bukata har ma a yankunan karkara da ba su da isasshen ilimi ta yadda za su bunkasa su ma.
Mun kuma gano cewa idan ka tallafawa mace daya to tamkar ka tallafawa dukkan karkarar ne, saboda shi namiji idan ka tallafa masa to daga baya barinka zai yi ya je ya nemi wani aikin a wani wajen daban.
Saboda shi haka Allah ya yi shi yana bukatar yin gogayya da neman wani aikin da ya fi wanda yake yi.
Amma mata suna da jajircewa da tsayawa kan aikin da suka fara, kuma manyan masu kawo sauyi ne a al'umma, su kan koyar da maza da mata, kuma suna iya fara wata hobbasa don samar da wani abu na kimiyya.
Don haka IDB ya yarda kwarai da karfafawa mata saboda yana daga cikin al'adar al'umma a taimakawa mata.
Kuma za a yi hakan ne ta hanyar samar musu da hanyoyin da suka dace da damarmaki, sannan kuma dole a fahimci irin al'ummar da suka taso a ciki da al'adarsu da kuma girmama al'adar tasu da addininsu.
Kuma a samar musu da wadannan abubuwa a cikin al'ummarsu saboda abu mafi kyau da za a iya shi ne a ba su abubuwan da suka dace, sai a bar su su yi amfani da abubuwan ta yadda suke ganin ya fi dacewa a al'ummarsu, ba wai sai lallai an tilasta musu yin wani abun da al'adarsu ba ta yarda da shi ba kamar ilimi ko koya musu dabaru, a dai ba su kayan aikin sai a ga yadda za su yi amfani da nasu dabarun wajen yin abun da ya dace wanda zai amfani al'ummarsu.
Sannan kuma muna bayar da tallafin karatu ga mata da sanya kyaututtuka da samar musu da damarmaki da koyar da su salon shugabanci.
Tallafin karatun kuwa sun hada har da yin digiri na biyu da digirin-digirgir a kowanne fanni musamman ma fannnin injinya,saboda shi ne fannin da har yanzu ba mu da mata da yawa da suka kware kuma muna bukatar tallafawa mata ta wannan fannin saboda muna bukatar baiwarsu da kulawarsu.
Kuma ina so na bayar da misali, a lokacin da aka kirkiri balam-balam din da ke kare mutum a yayin da hadari ya afku a cikin mota, wato Airbag, yawancin wadanda suke da hannu a kirkirar maza ne, don haka sun kirkire ta ne kawai don maza a bangaren zaman direba, har sai zuwa lokacin da aka samu mace cikinsu sannan ta yi tunanin cewa ya kamata a yi wata balam-balam din a wajen zaman na kusa da direba.
Don haka muna bukatar mata da maza a kimiyya amma ko wanne da bangarensa. Don haka muna bukatar karfafawa mata sosai, muna da bukatar nuna damuwa ga matsalar mata da halin da suke samun kansu a ciki don kuwa wadannan manyan abubuwa ne da za su taimaka wajen ciyar da al'umma gaba.
Tambaya: Shugabanni daga kasashe daban-daban na neman tallafi daga IDB, amma a lokuta da dama tallafin ba ya kai wa ga matan da suke karkara a wadannan kasashe. Ta yaya ku ke tabbatar da cewa irin wannan tallafin ya isa gare su?
Amsa: Wannan matsala a gaskiya tana faruwa ba ma ga mata kawai ba, ana bayarda tallafi har ma ga mabukata amma ba zai kai wajensu ba.
Ana bayar da tallafin maganuguna da na abinci amma a wasu lokutan ba ya kai wa wajensu. Don haka a kokarin ganin tallafin ya cimma al'umma dole sai an bi matakan IDB na karfafawa mutane gwiwa.
Don haka muna kokarin ganin mun yi aiki tare da hada gwiwa da al'ummar da muke son tallafa kai tsaye da kuma jagororinsu. Don haka ba wai zuwa muke kai tsaye mu bai wa matan taimako ba, dole sai mun bi ta hannun shugabannin al'umma da duk wadanda suka dace.
Kuma na tabbata ko wanne shugaba zai so ya yi wa al'ummarsa abun kirki don haka dole mu yi aiki da su.
Don haka a yanzu muna aiki tukuru don samar da wata kafa ta intanet da za ta hada dukkan masu ruwa da tsaki don gano hukumomin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba da 'yan kasuwa wadanda za mu iya aiki da su don sanin hanyoyin da za a bi a yi aikin tare don kai wa gaci, ta yadda a duk lokacin da muke wani babban aiki za mu hada kai tare da su don samun nasara da kuma amfanar dukkan al'umma.
Source: BBC Hausa