Al'ummar kasar Indiya sun yi ca cikin bacin rai kan wasu kalamai da ministan lafiya na jihar Assam ya yi cewa: 'cutar kansa wata ukuba ce daga Ubangiji sakamakon zunuban da mutum ya yi a baya.'
Himanta Biswa Sarma ya ce mutane na kuma iya kamuwa da cutar kansa sakamakon zunuban da iyayensu suka aikata.
Masu fama da cutar kansa da 'yan uwansu dai sun yi matukar bakin ciki da kalaman ministan.
Jam'iyyun adawa sun bayyana kalaman nasa da cewa 'abun takaici' ne sun kuma bukaci ya nemi gafarar al'umma a bainar jama'a.
Babbar jam'iyyar adawar jihar wato All India United Democratic Front, ta ce Mista Sarma ya yi wadannan kalamai ne saboda gazawarsa wajen kare yaduwar cutar kansa a jihar.
Ya yi wadannan kalaman ne a yayin da yake jawabi a wajen wani taro a Guwahati ranar Laraba.
"Ubangiji yana hukunta mu idan muka yi zunubi. A wasu lokutan a kan ga matasa maza zun kamu da cutar kansa ko su yi hatsari.
"Idan ka yi duba kan ko me ya sa hakan ya far
Kalaman nasa dai sun fusata masu amfani da shafin Twitter.
Sumita Sharma ta ce: "Ban cika son yin rubutu a Twitter kan abun da ya shafi rayuwata ba. Amma dole na fadi wannan - 'yar yayana ta rasa mahaifinta tana da shekara 11 sakamakon kansa. Mutane da dama sun rasa ransu saboda wannan cuta. Bana yi wa ko makiyana fatan su kamu da ita. Ka ji kunya Mista Minista."
Rekha Rao ta rubuta cewa: "Wannan abun takaici ne. Na rasa mahaifiyata sakamakon kansa. Ita ce wacce na fi so da girmamawa, ba mai zunubi ba kamar yadda ka bayyana masu cutar kansa. Wadannan kalamai naka cin mutunci ne ga masu fama da cutar da masoyansu
Geeta Sharma ta rubuta cewa: "Abun kunya ne yadda 'yan siyasa ke amfani da kalamai mara sa dadi, inda suke karawa masu fama da cutar kansa radadi. Ina addu'ar Allah ya sa su gane ya ba su hikimar iya kalamai."
Daga baya dai Mr Sharma, wanda dan jam'iyya mai mulki ta Bharatiya Janata Party (BJP) ne, ya yi kokarin kare kansaa Twitter din, al'amarin da bai gyara komai ba sai ma sake dagula rayukan mutane.
Ga abun da Mista Sharma ya rubuta a Twitter: Shin an gaya muku jawabina a kan cutar sankara na yi shi? Wa ya gaya muku? Na bukaci wasu sabbin jerin malamai su yi aiki ne da gaskiya kuma wa marasa galihu. A wannan yanayin na ce idan ba mu yi aiki da gaskiya ba a lahira za mu iya fuskantar nakasa da ka iya janyo azaba. Mene ne abun rashin tausayi a nan?"
Wani bincike da Cibiyar Binciken Lafiya ta Indiya ICMR ta yi ya ce, rashin wayar da kai da kuma yin gwaji na nufin kashi 12.5 cikin 100 ne kawai na marasa lafiya ke zuwa neman magani a matakin farko na cutar kansa.
Rahoton ya kara da cewa nn kiyasta cewa yawan masu fama da cutar kansa a kasar zai karu da kashi 25 cikin 100 nan da shekarar 2020.
Source: BBC Hausa
Title :
Zunubi Ne Ke Jawo Cutar Kansa-Ministan India
Description : Al'ummar kasar Indiya sun yi ca cikin bacin rai kan wasu kalamai da ministan lafiya na jihar Assam ya yi cewa: 'cutar kansa wata uku...
Rating :
5