Kwandasta na motocin bas a jihar Legas za su fara saka kaya na bai daya (inifom) daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2018.
An bullo da wannan tsari ne domin kyautata aikin nasu da kuma tabbatar da tsaro.
Shugaban kungiyar kwandastoci ta Najeriya BCAN, Isreal Adeshola, shi ne ya bayyana hakan a Legas.
Adeshola ya ce suna so su yi amfani da inifom din ne domin a tabbatar da kyakkyawan tsari a jihar da ma kasar baki daya.
Ya ce kungiyar ta riga ta fara horar da mambobinta da ke Legas domin a koya musu aikin kwandasta da kuma yadda ya kamata halayyarsu ta kasance.
Horaswar dai tana son ta tabbatar da cewa yaran motar suna da kyakkyawar hulda da masu hawa motocinsu.
Ya ce fara saka inifom din wanda ko wanne ke da lamba don tantancewa, zai sa kwandastoci a jihar su mayar da hankali da taka-tsan-tsan a ayyukansu.
Adeshola ya kara da cewa kungiyar na kokarin korar yara kanana masu aikin kwandasta a kasar.
Ya ce mutanen da suka fi shekara 18 da haihuwa nekawai za su iya shiga kungiyar.
Ya ce idan aka samu wani yaro yana aikin kwandasta, to za a kama shi.
Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya ce kaddamar da inifom din zai inganta fannin sufurin kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Yaran Mota Zasu Farasa Inifom Iri Daya A legas
Description : Kwandasta na motocin bas a jihar Legas za su fara saka kaya na bai daya (inifom) daga ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2018. An bullo d...
Rating :
5