Kimanin 'yan wasan Real Madrid 14 ne za su wakilci kasashensu a gasar kofin duniya da za a buga a Rasha a 2018.
Tun farko an tabbatar da 'yan wasa 11 na Real Madrid da kasashensu suka samu tikitin shiga gasar da za a yi a badi, a ranar Asabar ne Morocco ta samu tikitinta, inda Achraf Hakimi ke buga wa tawagar wasa.
Sauran 'yan wasa biyu da suka rage sune Luka Modric da Mateo 'yan kwallon Croatia, wadanda suke buga wasan cike gurbi da Girka, a karon farko Croatia ce ta yi nasara da ci 4-1, za kuma su buga wasa na biyu a ranar Lahadi.
Ga jerin 'yan kwallon Madrid da za su buga kofin duniya:
Spain: Ramos da Isco da Asensio da Carvajal da kuma NachoBrazil: Marcelo da kuma CasemiroPortugal: Cristiano RonaldoJamus: Toni KroosFaransa: Raphael VaraneCosta Rica: Keylor NavasMorocco: Achraf HakimiCroatia: Luka Modric da kuma Mateo Kovacic
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Madrid 12 Ne Zasu Buga Wasan Kofin Duniya
Description : Kimanin 'yan wasan Real Madrid 14 ne za su wakilci kasashensu a gasar kofin duniya da za a buga a Rasha a 2018. Tun farko an tabbatar d...
Rating :
5