Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai harin a wani masallaci da gidajen yan gudun hijira a yankin Muna Garage da ke wajen birnin Maiduguri a Arewa maso Gabashin Najeriya
Akalla mutum 16 ne suka mutu, wasu 22 suka ji raunuka, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno.
Wannan lamari ya faru ne bayan da 'yan kunar-bakin-wake guda 4, maza 2 da mata 2 suka tayar da bama-bamai.
Sun kai harin yankin Muna Garaje mashigar birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewacin Najeriya.
Maharan sun kai farmaki ne kan wani masallaci na 'yan gudun hijira da kuma gidaje .
Akasarin wadanda abin ya ritsa da su tsoffi ne da kananan yara kusan 7 masu shekara 5 zuwa 6.
Jagoran hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno, Alhaji Ahmed Satomi shi ya tabbatar da wadannan alkaluma.
Wadanda suka samu raunuka na ci gaba da samun kulawa ta musamman a asibiti.
Hukumomin jihar Borno da kuma kungiyar agaji ta Red-Cross ko kuma Croix -rouge su ne suka dauki nauyin yi masu magani.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Kunar Bakin Wake Sun Hallaka Mutum 12 A Borno
Description : Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai harin a wani masallaci da gidajen yan gudun hijira a yankin Muna Garage da ke wajen birnin Maiduguri ...
Rating :
5