Rundunar sojin Najeriya ta umarci jami'anta da su koyi manyan harsunan kasar uku.
Harsunan dai sun hada da Hausa da Yarbanci da kuma Igbo.
Mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Birgediya Sani Usman Kuka-sheka, ya ce manufar wannan umarnin shi ne samun isasshiyar sadarwa tsakanin sojoji da kuma al'umomin kasar.
Kazalika, Birgediya Kukasheka ya ce sabuwar dokar za ta taimaka wajen tattara bayanan sirri da kuma inganta dangantaka tsakanin sojoji da fararen hula.
Har wa yau ya ce dokar za ta inganta fahimtar juna a wajen aiki tsakanin sojojin kasar.
Kawo yanzu dai Turancin Ingilishi ne harshen da ake amfani da shi a Najeriya a hukumance.
Wannan sabuwar dokar tana nufin cewa za a yi ta amfani da harsunan Hausa da Yarbanci da kuma Igbo a lokacin da sojoji ke mu'amala da fararen hula ciki har da lokacin bincike da tambayoyi.
Najeriya dai tana da kimanin harsuna 250.
Kawo yanzu dai rundunar sojin kasar ba ta bayyana yadda za ta kaddamar da dokar a kasa irin Najeriya da ke da harsuna da yawa ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Yakamata Sojojin Nijeriya Su Koyi Hausa, Yarbanci Da Igbo
Description : Rundunar sojin Najeriya ta umarci jami'anta da su koyi manyan harsunan kasar uku. Harsunan dai sun hada da Hausa da Yarbanci da kuma Ig...
Rating :
5