Tukur Abubakar, wani mai nakasa ne da ke koya wa masu lafiya da nakasassu aikin hada takalma a kauyen Karmajiji da ke Abuja.
A lokacin da yake yaro, Tukur Abubakar ya yi fama da cutar Polio wadda ta nakasa kafafunshi kuma ta sa a yanzu yake tafiya da hannunsa na hagu da kuma na dama cutar ta dan taba.
Tukur ya shaida min cewa nakasarsa ba ta taba sa shi sha'awar bara ba.
Yadda gurgu ke koya wa masu kafa sana'a a Abuja
Maimakon hakan, ya fi mayar da hankali ne kan yadda zai samu na kansa.
Da na ziyarci shagonshi na langa-langa da ke karmajiji, wadanda suke koyan aiki a wajensa sun zauna cikin inuwar gaban shagonsa suna kallon shi yana koya musu aiki.
Tukur Abubakar yana juya keken dinkinsa da hannunsa na dama wanda cutar Polio ta nakasa.
Yana dinka igiyar wani sabon takalmin da yake hadawa ne.
Yana dan tsayawa lokaci-lokaci domin ya bayyana wa masu koyan aiki su bakwai da ke zaune cikin inuwar gaban shagonsa, yadda yake aiki.
Sai dai a shagonsa Tukur ana fuskantar kalubale da ya dara aiki da tsohon keken tafi-da-gidanka.
Dole ya hau boris din guragu domin ya je shagon cajin waya, inda zai samu wutar lantarki ta janareto wanda zai yi amfani da shi wajen tayar da injin goge gefen takalman da ya hada.
Me ya sa mai kafa zai koyi aiki a wurin mara kafa?
Daya daga cikin masu lafiyar da Tukur ke koya wa aiki, Aminu Adamu, ya ce suna koyar aikin ne domin su ma su samu hanyar dogara da kansu nan gaba.
Tukur ya ce shi ma yana matukar son ya ga mutane sun dogara da kansu domin a ganinsa yawan rashin aikin yi ne yake jaw
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Gurgu Yakoya Wa Masu Kafa Hada Takalmi
Description : Tukur Abubakar, wani mai nakasa ne da ke koya wa masu lafiya da nakasassu aikin hada takalma a kauyen Karmajiji da ke Abuja. A lokacin da y...
Rating :
5