Tsohon kociyan Manchester United David Moyes ya fara aikinsa da West Ham da rashin nasara, inda Watford a gidanta ta doke su da ci 2-0, a wasansu na Premiermako na 12, ranar Lahadi.
Fatan Moyes dan yankin Scotland, na samun nasara a wasansa na 500 a matsayin kociya ya gamu da cikas a sakamakon kwallon da Will Hughes ya ci a kashin farko na wasan a minti na 11.
Sai kuma ta biyu wadda mai tsaron ragar West Ham din kuma golan Ingila Joe Hart, ita ma ta daga ragarsa ta hannun Richarlison a minti na 64, abin da ya kai ga zaman sabuwar kungiyar kociyan a cikin ukun karshe masu faduwa daga gasar ta Premier, lamarin da ya kara nuna masa irin jan aikin da ke gabansa.
Ba shakka David Moyes ba zai ji dadin yadda alkalin wasa ya yi burus da laifin taba kwallon da hannu da aka yi ba kafin a ci su ta biyu, sannan kuma ga asarar dan wasansa na gaba na fam miliyan 25, Marko Arnautovic, wanda ya ji ciwo a hannu, a kashi na biyu na wasan.
Nasarar ta sa yanzu Watford tana matsayi na takwas da maki 18, yayin da West Ham din take ta 18 da maki tara a teburin na Premier.
Source: BBC Hausa
Title :
Watford Ta Doke Westham
Description : Tsohon kociyan Manchester United David Moyes ya fara aikinsa da West Ham da rashin nasara, inda Watford a gidanta ta doke su da ci 2-0, a w...
Rating :
5