Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta ce mutumin da ya fallasa kudin da aka gano a wani gida a unguwar Ikoyi da ke jihar Legas "ya zama miloniya."
Shugaban riko na hukumar, Ibrahim Magu, ne ya tabbatar da haka a wani taro a birnin Vienna na kasar Australiya, in ji sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya fitar.
Uwujaren ya tabbatar wa BBC cewa hukumar ta bai wa wanda ya fallasa boye wadansu makudan kudade a wannan gida, amman ya ki ya bayyana nawa aka bai wa mutumin.
A shekarar da ta wuce ministar kudin Najeriya, Kemi Adeosun, ta bayyana shirin gwamnatin kasar na bayar da tukuicin kashi biyar cikin 100 ga duk wanda ya fallasa "haramtaccen kudin" da ake zargin na sata ne.
Idan aka yi la'akari da cewa kudin da aka samu a gidan na Legas a farkon shekarar nan ya kai naira biliyan 13, za a iya cewa wanda ya kwaramata bayanin kudaden zai samu kimanin naira miliyan 650 (kashi 5 cikin 100 na kudin da aka samu a cikin wani bene a Legas).
Bayan hukumar EFCC ta yi wawan kamun ne dai aka gano cewa kudaden suna da alaka da tsohon shugaban hukumar leken asirin Najeriya ta NIA, Ayo Oke.
Wannan ya sa shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sa aka dakatar da Mista Oke daga farko, kuma ya kore shi daga baya.
Source: BBC Hausa
Title :
Wanda Ya Fallasa Dalolin Da EFCC Ta Gano A Legas Ya Zamo Miloniya
Description : Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta ce mutumin da ya fallasa kudin da aka gano a wani gida a un...
Rating :
5