Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi bayan dan takarar majalisar dattijai da ke cikin tsaka mai wuya daga jihar Alabama kan zargin nuna ƙulafuci kan 'yan mata.
Ya nunar cewa Mista Roy Moore "gaba daya ya musanta" aikata badala da jerin wasu 'yan mata, ciki har da 'yar shekara 14, lokacin da yake kan ganiyar samartakarsa.
"Ba ma bukatar mutum mai matsakaicin ra'ayi a can, wani dan jam'iyyar Dimokrat," Mista Trump ya ce game da zaben da za a yi watan gobe.
Fadar White House a baya ta ambato Shugaba Trump na jin cewa zarge-zargen da ake yi wa Moore na da "tayar da hankali matuka."
Sai dai a ranar Talata, Mista Trump ya caccaki abokin takarar Roy Moore dan jam'iyyar Dimokrat, Doug Jones, wanda a yanzu ra'ayin jama'a ya nuna cewa yana kan gaba da kashi 47% a kan abokin fafatawarsa mai kashi 42%.
"Na ga tarihinsa, shi mutum ne dan kan katanga," Mista Trump ya fada daidai lokacin da yake barin White House a kan hanyarsa ta tafiya hutun kwana biyar a Florida.
Shugaban Amurkan ya kuma nuna goyon bayansa ga dumbin matan da ke fitowa fili da zarge-zargen an neme su da lalata tun bayan tonon sililin da aka yi wa fardusan shirya fina-finan Hollywood Harvey Weinstein a watan jiya.
"Mata na da daraja ta musammam," a cewar Trump.
"Ina jin wannan lokaci ne na musammam, dumbin abubuwa na fitowa fili kuma ina jin hakan abu ne mai kyau ga al'ummarmu kuma abu ne mai kyau sosai, yana da kyau sosai ga mata don haka ina farin ciki."
Donald Trump shi da kansa ya fuskanci zarge-zargen yin lalata da dama a lokacin yakin neman zabensa bara, amma dai ya musanta.
Tsare-tsaren shugaban kasar dan jam'iyyar Republican a zauren majalisar dattijan Amurka ka iya shiga wani hali, idan aka kayar da Roy Moore a zaben 12 ga watan Disamba - 'yan Republican na da kankanin rinjaye a majalisar dattijai da kujera 52 a kan 48.
Source: BBC Hausa
Title :
Trump Yakare Wadanda Ake Zargin Su Da Tumurmusa 'Yan Mata
Description : Shugaban Amurka Donald Trump ya goyi bayan dan takarar majalisar dattijai da ke cikin tsaka mai wuya daga jihar Alabama kan zargin nuna ƙula...
Rating :
5