Sojojin Zimbabwe sun karanta wata sanarwa a gidan talbijin din gwamnatin kasar, ZBC, inda suka ce sun dauki matakin ne don "maganin miyagu".
Sai dai sun ce wannan ba "juyin mulkin soja ba ne" kuma Shugaba Robert Mugabe yana nan lafiya.
Cikin dare an ji amon harba manyan bindigogi da atilare a yankunan arewacin birnin Harare.
Sojojin suka ce suna son su yi maganin wadanda "ke tafka aika-aikar da ta tsunduma kasar cikin wahalar rayuwa da matsin tattalin arziki.
"Kuma da zarar mun kammala aikinmu, muna sa ran cewa harkoki za su koma kamar yadda aka saba."
Sanarwar ta ce Shugaba Mugaba dan shekara 93 da iyalinsa suna nan lafiya kuma akwai tabbcin tsaronsu.
An ji gagarumar karar fashe-fashen manyan bindigogi a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, inda sojoji suka mamaye shalkwatar yada labaran kasar, ZBC.
An ga motoci masu sulke a kusa da tsakiyar birni. Tun da farko, jakadan Zimbabwe a Afirka ta Kudu, Isaac Moyo ya yi watsi da rade-radin juyin mulki, ya ce har yanzu gwamnati "na nan lafiya".
A ranar Talata ce jam'iyyar Zanu-PF ta Zimbabwe ta zargi babban hafsan sojin kasar da tunzura bore bayan ya ce rundunar soja a shirye take ta shiga tsakani don kawo karshen rikicin siyasa.
Wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar na bayyana kalaman Janar Constantino Chiwenga a matsayin wani abin mamaki da firgitarwa kuma cin amanar kasa.
Babu dai wani martani daga bakin shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe dan shekara 93 a duniya.
Janar Constantino Chiwenga ya kalubalanci Shugaba Mugabe bayan ya kori mataimakinsa daga kan mukaminsa.
Sojoji sun fada wa ma'aikata a tashar yada labaran gwamnatin kasar cewa "kada su damu", wata majiya ta kara da cewa, kuma sun je ne kawai don su kare ginin.
Wakiliyar BBC a Harare Shingai Nyoka, ta ce an ji amon manyan bindigogi da atilare a unguwannin arewacin birnin, inda wasu manyan jami'an gwamnati ciki har da shugaban kasar ke da zama.
Ofishin jakadancin Amurka a Harare ya aika wani sakon tiwita cewa "saboda rashin tabbas din da ake ciki" ba zai bude ba ranar Laraba.
Ya kuma shawarci Amurkawan da ke Zimbabwe su "nemi wurin fakewa" har zuwa lokacin da za su ji sanarwa ta gaba.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tana "bibiya kut-da-kut" halin da aka shiga a Zimbabwe kuma ta bukaci dukkan bangarori su warware dambarwarsu cikin "lumana da kwaciyar hankali".
Source: BBC Hausa
Title :
Sojoji Sun Mamaye Gidan Talbijin Din Zimbabwe
Description : Sojojin Zimbabwe sun karanta wata sanarwa a gidan talbijin din gwamnatin kasar, ZBC, inda suka ce sun dauki matakin ne don "maganin miy...
Rating :
5