A duk lokutan da aka shafe inda tattalin arzikin Zimbabwe ya yi ta tabarbarewa tsawon shekaru, an sha hasashen durkushewar Robert Mugabe ta fuskar siyasa da ma ta lafiya, sai dai ya tsallake wannan fata, har sai yanzu da wani abu ya faru.
Haka kuma, ana ganin kamar ya wuce gona da iri wajen ganin cewa matarsa ta gaje shi, hakan ne kuma ta sa shugabannin soji wadanda da bazarsu yake rawa a mulkin, suka daina ba shi goyon baya.
Halin lafiyarsa dai ya ci gaba da tabarbarewa cikin shekarun da suka gabata, kasancewar sa dan shekara 93, duk da cewa a hukumance ya yi aniyar sake tsayawa takara.
Kafin zaben shekarar 2008, ya ce: "Idan ka fadi zabe kuma mutane suka juya maka baya, to lokacin barin siyasa ya yi."
Amma bayan da Morgan Tsvangirai ya yi nasara a kansa, sai Mista Mugabe ya fiddo wasu halaye da suka saba da maganar tasa, inda ya yi rantsuwa cewa 'Allah ne kadai' zai iya tsige shi daga ofis.
Amma don ya tabbatar da ikon nasa, sai ya dinga amfani da rikici.
Shi kuwa Mista Tsvangirai a kokarinsa na kare magoya bayansa, sai ya janye daga zagaye na biyu, amma duk da haka an tilasta Mista Mugabe ya sanya Mista Tsvangirai a matsayin mataimakinsa, shi kuma ya ci gaba da mulkin da ya fara tun shekarar 1980.
Babban abun da ya sa Mista Mugabe ya yi suna shi ne yakin da aka yi a shekarun 1970.
Tarihin rayuwar Robert Mugabe 1924: Shekarar da aka haife shiAn horar da shi a matsayin malami1964: Gwamnatin Rhodesia ta daure shi1980: Ya lashe zaben da aka yi bayan 'yancin kai1996: Ya auri Grace Marufu2000: Bai yi nasara ba a zaben raba-gardamr da aka yi ba na karfin ikon shugaban kasa da kuma hana Turawa mallakar gonaki2008: Ya zo na biyu a zagayen farko na zaben da suka fafata da Tsvangirai, wanda ya janye saboda harin da aka kai kan magoya bayansa2009: Ya rantsar da Tsvangirai a matsayin firai minista a lokacin da ake fuskantar durkushewar tattalin arziki a kasar2016: An gabatar da takardun lamuni a yayin da karancin takardun kudya yi tsanani2017: Ya kori mataimakinsa da ya dade suna aiki tare wato Emmerson Mnangagwa
Jigo a juyin-juya hali
Akwai lokacin da ake yi masa kallon wani jigo a juyin-juya hali, inda yake fada da tsirarun Turawa don neman 'yancin al'ummarsa - wannan ne dalilin da ya sa shugabannin Afirka da dama suke sako-sako wajen sukar sa.
Tun bayan da Zimbabwe ta samu 'yancin kai, an samu ci gaba a duniya, amma shi har yanzu tunaninsa na zamanin da ne.
Har yanzu jaruman yakin kwato yanci na jam'iyyar Zanu-PF na yakar munanan akidun jari hujja da mulkin mallaka.
A kan yi watsi da masu suka ana kwatanta su da maciya amana, abin da ke tunowa da yakin sari-ka-noke, lokacin da alakanta mutum da wannan kalmar tamkar hukuncin kisa ne.
Ya sha dora alhakin matsin tattalin arzikin da Zimbabwe ke fama da shi a kan kasashen yamma, karkashin jagorancin Birtaniya, don hambarar da shi saboda kwace gonakin Turawa da ya yi.
Masu sukarsa na yawan zargin sa da cewa ba ya nuna damuwa kan yadda tattalin arzikin zamani ke aiki.
Ya fi mayar da hankali kan tambayar yadda za a raba zarikin kasa, maimakon neman hanyar da za a inganta shi.
Mr Mugabe ya taba cewa tattalin arzikin kasar da zai taba durkushewa gaba daya ba, kasancewar kasarsa ta fuskanci matsalar tattalin arziki mafi kamari a duniya, da kuma hauhuawar farashi da ya taba kai wa kashi miliyan 231 a watan Yulin 2008, kai ka ce yana so ne ya gwada ikirarin nasa.
Farfesa Tony Hawkins na jami'ar Zimbabwe ya taba fuskantar wani abu tattare da shugaban Zimbabwe, inda ya ce: "A duk lokacin da batun tattalin arziki ya hadu da siyasa, to siyasa ce ke yin nasara."
A shekarar 2000, ya fuskanci kakkarfar hamayya a karon farko, ya damalmala tattalin arzikin kasar don samun karfin iko a siyance.
Ya kwace gonakin Turawa wadanda su ne kashin bayan tattalin azrikin kasar, ya kuma fatattaki kungiyoyin tallafi, wato dai cikin siyasa Mista Mugabe ya yi wa makiyansa shigar-burtu - ya ci gaba da kasancew a mulki.
Source: BBC Hausa
Title :
Shin Mugabe Jarumine Ko Mai Laifi
Description : A duk lokutan da aka shafe inda tattalin arzikin Zimbabwe ya yi ta tabarbarewa tsawon shekaru, an sha hasashen durkushewar Robert Mugabe ta ...
Rating :
5