Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce a watan Janairu, za a fara nazarin da aka dade ana jiran ganin an yi na ko akwai alaka tsakanin buga kwallon kafa da ka da kuma raunin kwakwalwa.
Likitan da ya yi ikirarin cewa tsohon dan wasan gaba na kungiyar Westbromwich Albion da kuma tawagar Ingila Jeff Astle, ya mutu ne saboda matsalar kwakwalwa da ya samu ta hanyar yawan buga kwallo da ka, shi ne zai jagoranci binciken.
Binciken da aka yi a kan musabbabin mutuwar dan wasan a 2002 ya nuna cewa yawan buga kwallon kafa wadda ke da nauyi da ka shi ne ya haddasa masa raunin kwakwalwar.
Dakta Willie Stewart ya ce rahoton da zai fitar bayan nazarin zai yi kokarin nuna irin illar wasan kwallon kafa da kan samu masu buga ta da ka a bayan tsawon lokaci, nan da shekara biyu zuwa uku.
Hukumar kwallon kafa ta Ingila da kuma kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa ta Ingila, su ne suka ba wa Dakta Stewart aikin binciken.
Source: BBC Hausa
Title :
Shin Buga Kwallo Da Kwalkwal Nayi Wa Kai Illa?
Description : Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce a watan Janairu, za a fara nazarin da aka dade ana jiran ganin an yi na ko akwai alaka tsakanin buga kw...
Rating :
5