Shugaban kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya ce a bayanne take cewa Saudiyya ce ta tilastawa Sa'ad Hariri yin murabus.
Jagoran kungiyar ta Hezbollah da ke Lebanon ya zargi Saudiyya da ayyana yaki kan kasarsa, bayan wasu kwanaki da fira ministan Lebanon Saad al Hariri ya yi shellar ajiye mukaminsa a Riyahd babban birnin kasar Saudiyyar.
Hassan Nasrallah ya ce Saudiyya na rike da Mr Hariri ne ba tare da amincewarsa ba.
Ya kuma zargi Saudiyya da ruruta wutar rikici tsakanin Israila da Lebanon.
Kungiyar Hezbollah mai karfin fada a ji abokiyar Iran ce, wadda take zargin Saudiyya da haddassa zaman doya da manya a Lebanon da kuma yankin baki daya.
A wani jawabi da aka nuna kai tsaye a Riyadh a ranar Asabar, Mr Hariri ya ce zai ajiye mukaminsa saboda barazanar da ake yi ma rayuwarsa.
Ya kuma soki Hezbollah da Iran.
Sai dai shugaban kasar Lebanon, Michel Aoun da kuma wasu jiga jigan yan siyasa sun nemi ya dawo gida ya yin da ake zargin cewa Saudiyya ta yi masa daurin talala kuma ita ce ta tilasta masa ya bada kai domin bori ya hau.
Source: BBC Hausa
Title :
Saudiyya Na Takalar Lebanon-Hezbollah
Description : Shugaban kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya ce a bayanne take cewa Saudiyya ce ta tilastawa Sa'ad Hariri yin murabus. Jagoran kung...
Rating :
5