Ana ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a yammacin kasar Saudiyya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum biyu, ya kuma jawo an rufe makarantu da dama.
Lamarin ya fi munana a birnin Jidda, inda matuka mota da babura suka makale.
Hukumar kare lafiyar al'ummar kasar ta ce jami'ansu sun ceto mutum kusan 500.
Kafar yada labaran intanet ta Saudi Gazette ta ce hukumar lafiya ta Jidda ta karbi rahotannin gaggawa 29, inda takwas daga cikinsu ke da alaka da wadanda lantarki ya ja su.
Sauran kuma sun faru ne sakamakon hadurra a kan tituna.
Saudi Gazette ta kuma ce hukumar ba da agaji ta Red Crescent a Madina, ta ruwaito cewa mutum 17 ne suka zame suka fadi a kusa da masallacin Manzon ALlah SAW da kuma tsakiyar birnin.
An ceto mutum kusan 481 wadanda suka makale a Makkah da Madina da Tabuk da Al-Jouf.
An kwashe iyalan gida 10 da kuma ababen hawa 41.
Kafafen yada labarai a Saudiyya sun kwatanta ambaliyar ta bana da irin wacce Jiddah ta fuskanta a shekarar 2009, inda sama da mutum 100i suka mutu, yayin da gwamnatin kasar kuma ke ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa.
Source: BBC Hausa
Title :
Saudiyya Na Fuskantar Ambaliyan Ruwa
Description : Ana ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa a yammacin kasar Saudiyya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum biyu, ya kuma jawo an r...
Rating :
5