Wani dan asalin yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna a Najeriya ya ce manoma a yankinsu kan shiga tasku lokacin jido amfanin gonakinsu saboda yawan satar mutane.
Zubairu Abdurra'uf ya ce dole sai manomi ya fanshi kansa ko kuma a yi garkuwa da shi har sai danginsa sun biya fansa.
"Idan ka taso tun daga cikin Kaduna kana fitowa daga filin jirgin sama kafin ka kai Buruku har Birnin Gwari, wannan dajin duk suna nan," in ji shi.
Ya ce shi ya sa wannan hanya ta Kaduna zuwa Legas ta yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane.
Yankin Birnin Gwari da kan hanyar Kaduna zuwa Abuja na daga cikin sassan da suka fi fama da sace-sacen mutane don neman kudin fansa.
Wannan lamari ne ya sa mutanen kauyen Sabon Gayan a kan titin Abuja zuwa Kaduna suka gudanar da wata zanga-zanga ranar Lahadi, don nuna damuwa kan karuwar ayyukan masu satar mutane.
A cewar Zubairu Abdurra'uf, ko kasuwa manomi ya kai hatsinsa ya sayar, to sai an bi shi gida ya bayar da kudin cinikinsa.
Ya ce: "Har fulani su kansu ba a bar su ba, ana sace matansu a ce sai sun sayar da shanu sun biya fansa kafin a sako su."
Ya yi zargin cewa masu garkuwa da mutanen suna hada baki da wasu da ke tsegunta musu bayanai game da matafiya a tashoshin mota a cikin Kaduna.
"Akwai wurare guda biyu, in ba jami'an tsaro sun yi kokarin sun tayar da irin wadannan mutane ko sun kama su ba, to har yanzu ba a rabu da Bukar ba kenan," a cewarsa.
Ya ce rashin 'yan sanda a kan titunan yankunansu dare da rana na daga cikin dalilan da suka sa matsalar ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa.
Zabairu Abdulra'uf wanda kuma shi ne, Dan masanin Birnin Gwari, ya ce kafa kungiyoyin sintiri tsakanin al'ummomin wadannan yankuna da kuma samun hadin kan jami'an tsaro ne zai taimakawa matuka wajen shawo kan matsalar satar mutane don neman fansa.
Source: BBC Hausa
Title :
Sai Ankafa Civilian JTF Kan Masu Satar Mutane
Description : Wani dan asalin yankin Birnin Gwari cikin jihar Kaduna a Najeriya ya ce manoma a yankinsu kan shiga tasku lokacin jido amfanin gonakinsu sab...
Rating :
5