A ranar Lahadi ne budurwar dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ta haifa masa 'ya mace a birnin Madrid na Spaniya.
Georgina Rodriguez da Ronaldo sun saka wa yarinyar suna Alana Martina, kuma ita ce ta farko da ya haifa tare da wannan budurwa tasa.
A watan Yuni ne Ronaldo ya haifi tagwaye wadanda aka bai wa suna Eva da kuma Mateo, kuma da ma dai yana da Ronaldo Junior mai shekara bakwai.
Ronaldo, wanda shi ne kyaftin din Portugal, yana hutu yanzu haka, bayan da tawagar Portugal ta amince ya ziyarci budurwar tasa, yayin da ake hutu a gasar Spaniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Ronaldo Yazama Uban 'Ya'ya Hudu
Description : A ranar Lahadi ne budurwar dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ta haifa masa 'ya mace a birnin Madrid na Spaniya. Georgina Rodr...
Rating :
5