Cristiano Ronaldo ya kara kafa wani tarihi a gasar kofin Zakarun Turai bayan da zakarun, Real Madrid suka lallasa Apoel Nicosia 6-0, suka kai mataki na gaba na kungiyoyi 16.
Ronaldo ya ci biyu ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, abin da ya sa yanzu yake da kwallo 18 a gasar zakarun Turan a 2017, mafi yawa a shekara daya.
Luka Modric ne ya fara bude cin a minti na 23, sai Benzema ya biyo baya a minti na 39, minti biyu tsakani Nacho ya jefa tasa, sai kuma Benzema ya kara ana shirin tafiya hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo ne minti hutu da shiga fili sai Ronaldo ya ci tasa ta farko, can kuma a minti na 54 ya kara.
Ronaldo ya kasance dan wasa na uku a zamanin gasar zakarun Turai da ya ci bal a kowane wasa biyar na farkon gasar.
Ya ci kwallo 18 a wasa goma da ya yi a gasar, wanda hakan ya sa yanzu yana da jumllar kwallo 113, inda ya wuce dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi da 16.
Kasancewar Tottenham ta zama ta daya a rukunin nasu na takwas (Group H), Real Madrid kenan za ta hadu da wata kungiyar ta daya a zagaye gaba na sili-daya-kwale, tun da ita ce ta biyu.
Nasarar da Tottenham ta yi a gidan Dortmund 2-1 ta sa kungiyar ta Premier ta zama jagora a rukunin duk da sauran wasa daya da ya rage.
Zinedine Zidane ya dauki kofin na zakarun Turai a kaka biyu da ya yi yana jan ragamar Real, amma Barcelona ta yi musu rata da maki goma a gasar La Liga a karshen mako.
Source: BBC Hausa
Title :
Ronaldo Yakafa Tarihi A Wasan Zakarun Nahiyar Turai
Description : Cristiano Ronaldo ya kara kafa wani tarihi a gasar kofin Zakarun Turai bayan da zakarun, Real Madrid suka lallasa Apoel Nicosia 6-0, suka ka...
Rating :
5