Wata 'yar majalisar dokoki a jam'iyyar adawa ta Zimbabwe, Priscilla Mushonga ta ce rashin adalci ne a dora wa Grace Mugabe laifi kan kwaranyewar farin jinin mai gidanta.
A cewar Priscilla Mushonga: "Ina jin abu ne mai sauki a zargi mace laifi. Duk da yake, Shugaba Mugabe ya fara shiriricewa ne tun cikin 1983 lokacin da ya kashe mutum dubu 20 a yankin Matabeleland.
"Mai yiwuwa a lokacin Grace tana aji daya a sakandare."
A ranar Talata ce, Robert Mugabe ya yi murabus bayan shafe tsawon shekara 37 a kan karagar mulki, lamarin da ya janyo gagarumar murna da sowa a titunan Zimbabwe.
Murabus din dadadden shugaban dan gwagwarmaya ya zo ne bayan sojojin kasar sun dauki mataki, inda suka yi wa shi da mai dakinsa daurin talala a gidansa.
Priscilla Mushonga ta ce eh, tana iya kasancewa a tsakiyar harkokin mulki yanzu amma ita kawai karan kada miya ce da Mugabe ke amfani da ita don ci gaba da mulki.
"Don haka a dora komai a kan Grace, ina jin irin abin nan ne nuna son kan maza, kuma matukar raini ne ga jinsin mata."
Ana kallon Grace Mugabe a matsayin wadda shugaban yake kokarin ganin ta gaje shi a kan gadon mulki, inda ya yi murabus.
Mista Mugabe dai ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa saboda zargin rashin biyayyarsa, abin da ya harzuka matakin da sojojin suka dauka, har ta kai ga saukar Robert Mugabe daga mulki.
Yanzu al'ummar Zimbabwe na dakon komawar Emmerson Mnangagwa tsohon na-hannun daman Robert Mugabe, wanda ake sa rai za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar.
Wani mai magana da yawun jam'iyyar Zanu-PF ya ce Mista Mnangagwa zai karasa wa'adin Mugabe kafin a yi zabe na gaba, cikin watan Satumban 2018.
Wasu dai na tambayar ko mika mulki hannun Mnangagwa zai kawo wa kasar wani canji.
Source: BBC Hausa
Title :
Rashin Adalcine Zargin Grace Mugabe-Yar Majalisa
Description : Wata 'yar majalisar dokoki a jam'iyyar adawa ta Zimbabwe, Priscilla Mushonga ta ce rashin adalci ne a dora wa Grace Mugabe laifi kan...
Rating :
5