Bayan girgizar kasar da ya sanadiyar mutuwar mutum sama da 400 a Iran, gwamnatin kasar ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar makoki a duk fadin kasar.
Masu ceto sun shafe dare baki daya su na neman masu sauren shan ruwa a gaba da suka makale a cikin tarkace.
Duban 'yan kasar Iran da dama ne suke kwashe dare na biyu a fili Allah ta'ala, wato ba cikin mahalansu ba.
Sun kwashe daren na biyu a wani yanayi na iska mai sanhi da ke ke kadawa.
A kalla mutum sama da 400 ne suka mutu kuma wasu kusa 700 suka samu raunika daban -daban, sanadiyar girgizar kasar ta ranar lahadi.
Har dai cikin dari, masu cuto na ci gaba da neman mutanan da suka makkale a cikin tarkace a yankin gabashin kasar,musamman a yakin Kermanshah mai tsauni .
Gwamnati kasar ta Iran dai ta sanar da cewa wannan rana ta Talata, za ta kasance ranar makoki a cikin kasar baki daya.
Source: BBC Hausa
Title :
Ranar Zaman Makoki A Iran
Description : Bayan girgizar kasar da ya sanadiyar mutuwar mutum sama da 400 a Iran, gwamnatin kasar ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar makoki a duk ...
Rating :
5