Babban jam'iyyar adawa a Nijeriya PDP ta yi babban kamu a jihar Neja inda ta karbi 'ya'yan jam'iyoyi daban daban ciki har da 'ya'yan jama'iyar APC mai mulki kimanin mutum 817.
Jam'iyar tasamu wannan gagarumar karuwa ne a wani taron kaddamar da dan takaran sanata mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa a zaben 2019 Honorabul Muhammad Sani Duba da ya gudana a garin Kontagora cibiyar Neja ta Arewa, taron da ya samu halartan shugabannin jama'iyar na Jiha da kananan hukumomi takwas dake shiyyar.
Wadanda suka sauya shekar sun kona tsintsiya tare da baiyana cewar jam'iya ce maras alkibila wacce ba abunda ke cikinta sai tarin yaudara da alkawarurrukan karya wanda tunda aka zabeta ba abun azo agani da ta tsinanawa al'ummar Najeriya.
A nasa jawabin Honorabul Muhammad Sani Duba ya baiyana cewar "da farko ina godiya ga Allah ina kuma godiya ga daukacin 'ya'yan jam'iyyar PDP akan cancantar da suka ga na yi suka kirawo ni domin na yi takara, hakazalika galibin 'ya'yan jama'iyar PDP da suka sauya sheka a baya zuwa APC nan ba da dadewa ba za su dawo gida domin sun gane APC jam'iya ce maras alkibila, PDP ce kadai jama'iyar da 'yan Najeriya suka yarda da ita kuma takeda kishin cigaban kasar nan, domin damaman wadanda aka zaba a jama'iyar APC zaben tumun dare ne al'umma sukayi karkashin guguwar sakk, kuma gashi har 'yan Nijeriya sun fara jifan su, inji shi.
Title :
Photos: Jam'iyar PDP Ta Yi Babban Kamu A Jihar Neja
Description : Babban jam'iyyar adawa a Nijeriya PDP ta yi babban kamu a jihar Neja inda ta karbi 'ya'yan jam'iyoyi daban daban ciki har d...
Rating :
5