Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce dan wasansa na tsakiya Paul Pogba ajinsa daban, bayan da ya dawo wasa daga jinyar da ya yi, ya ci kwallo daya kuma ya bayar aka ci.
Dan wasan dan Faransa ya sanya wa Anthony Martial kwallon da ya farke wa Manchester United, sannan kuma ya ci ta uku, a wasan da United din ta farfado daga ci daya, ta doke Newcastle United 4-1 a Old Trafford, ranar Asabar.
Mourinho ya ce dan wasan wanda bai yi wa United wasan Premier da na kofin lig12 ba saboda jinyar raunin da ya ji a cinya ya taka rawa sosai a wasan da suka karbi bakunci.
Pogba mai shekara 24, shi ne ya kasance dan wasa mafi kwazo a karawar da ta sa United ta yi bajintar da ba ta taba yi ba, ta yin wasa 38 ba tare da an doke ta ba a Old Trafford, nasarar da ta sa ta ci gaba da kasancewa ta biyu da maki 26 a bayan Manchester City jagora a tebur da mai 34.
A wasan da suka yi da Newcastle din Mouriho ya sako Marouane Fellaini a minti na 70 ya maye Pogba.
Ranar ta kasance wa Man United ta farin ciki, domin tsohon dan wasan kasar Sweden Ibrahimovic, mai shekara 36, ya yi wasansa na farko tun bayan da ya ji rauni a guiwarsa ranar 20 ga watan Afrilu, inda ya taka leda tsawon minti 14.
Kididdigar alkaluman amfanin Pogba a wasannin Manchester United na kakar bana ta 2016-17.
Ya yi wasa 33, sannan bai taka mata leda a wasa 16 ba.
Kungiyar ta yi nasara a wasa 19 da ya buga mata, sannan a wasa 6 kawai ta yi nasara da ba ya nan.
Tana da kwallo 57 a lokacin da ya yi mata wasa, amma kuma 20 take da a lokacin da bai yi wasa ba.
Man United din ta yi nasara a kashi 57.6 cikin dari a lokacin wasannin da ya yi mata yayin da take da kashi 37.5 cikin dari na nasara, a lokacin da bai taka mata leda ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Paul Pogba Na Daban Ne-Mourinho
Description : Kociyan Manchester United Jose Mourinho ya ce dan wasansa na tsakiya Paul Pogba ajinsa daban, bayan da ya dawo wasa daga jinyar da ya yi, ya...
Rating :
5