Hukumomi a Najeriya sun ce sun sayo maganin dafin maciji, daga kasashen Birtaniya da Costa Rica bayan watanni ana fama da rashin maganin a asibitocin dake kula da masu fama da ciwon.
Fiye da mutum 200 sun rasa rayukansu a watan jiya daga sarar maciji saboda rashin maganin.
Yankunan da matsalar tafi kamari sun hada da Kaltungo dake jihar Gombe da Zamko dake jihar Filato, inda a kullum ake samun wadanda suka rasa rayukansu.
Jami'an kiwon lafiya sun ce an fara raba magungunan kimanin 5,000 ga cibiyoyin dake kula da wannan matsalar a cikin Najeriya.
Masana sun kiyasta cewa maciji na sarar fiye da mutum 10,000 a kowace shekara a Najeriya, kuma daruruwan mutane kan rasa rayukansu a sakamakon haka.
Saboda Najeriya bata iya samar da maganin macijin a cikin gida, ta kan aika da samfurin dafin macijin zuwa kasahen waje domin a hada maganin.
Source: BBC Hausa
Title :
Nijeriya Tashigo Da Maganin Maciji
Description : Hukumomi a Najeriya sun ce sun sayo maganin dafin maciji, daga kasashen Birtaniya da Costa Rica bayan watanni ana fama da rashin maganin a a...
Rating :
5