Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta Argentina 4-2 a wasan sada zumunta da suka buga a Rasha a ranar Talata.
Ever Banega ne ya fara ci wa Argentina kwallo a bugun tazara a minti na 28 da fara tamaula, sannan Sergio Aguero ya ci ta biyu a minti na 37.
Saura minti daya a je hutu ne Super Eagles ta zare kwallo daya ta hannun Kelechi Iheanacho a bugun tazara, bayan da aka dawo ne ta farke ta hannun Alex Iwobi, sannan ta kara ta uku ta hannun Brian Idowu.
Bayan da wasa ya yi nisa kuma saura minti shida a tashi daga karawar Alex Iwobi ya kara ta hudu kuma ta biyu da ya ci a fafatawar.
Argentina ta samu tikitin zuwa buga gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 daga Kudancin Amurka, yayin da Nigeria za ta wakilci Afirka daga biyar din da za su je Rasha daga nahiyar.
Source: BBC Hausa
Title :
Nijeriya Ta Lallasa Argentina Da kwallo 4 Da 2
Description : Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta doke ta Argentina 4-2 a wasan sada zumunta da suka buga a Rasha a ranar Talata. Ever Banega ne ya fara c...
Rating :
5