Najeriya tana mataki na 35 a rahoton kididdigar shekara-shekara kan yanayin gwamnatoci a nahiyar Afirka, wanda Gidauniyar Mo Ibrahim ta fitar a birnin Dakar na kasar Senegal ranar Litinin.
Kodayake rahoton ya ce gwamnatin Najeriya ta dan yi aiki a tsawon shekara biyar da suka wuce, kuma ta samu maki 48.1 cikin 100.
Sai dai abin da kasar ta samun ya yi kasa da adadin tsaka-tsaki na kasashen yankin Yammacin Afirka wato maki 53.8.
Har ila yau Najeriya ta samu maki mai yawa a bangaren Cudanya da kuma Kare hakkin dan Adam, inda ta samu maki 52.5.
Sai dai kuma ba ta samu maki mai yawa ba a bangaren Samar da Dama Mai Dorewa ta Fuskar Tattalin Arziki, inda ta samu maki 42.3 cikin 100.
Kasashen Cote d'Ivoire da Morocco da Namibiya da kuma Senegal sun samu ci gaba ta fuskar samar da shugabanci nagari.
Rahoton ya ce nahiyar Afirka tana bin matakan da suka dace wajen samar da shugabanci na gari "duk da cewa wadansu suna abin bai da ce ba".
"Afirka tana samun ci gaba sannu a hankali," in ji rahoton.
A bara dai nahiyar ta samu ci gaba wajen samar da shugabanci nagari, inda ta samu maki 50.8 cikin 100, a cewar rahoton.
Hamshakin dan kasuwan nan na kasar Sudan, Mo Ibrahim, shi ne ya kafa gidauniyar domin karfafa shugabanci nagari a nahiyar Afirka.
Source: BBC Hausa
Title :
Nijeriya Ne Na 35 A Afirka-Gidauniyar Mo Ibrahim
Description : Najeriya tana mataki na 35 a rahoton kididdigar shekara-shekara kan yanayin gwamnatoci a nahiyar Afirka, wanda Gidauniyar Mo Ibrahim ta fita...
Rating :
5