A ranar 3 ga watan Agustan 2017 ne Neymar ya koma Paris St-Germain daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya.
Dan wasan Brazil, mai shekara 25, ya fara buga wa PSG tamaula a karawar da za ta ziyarci Guingamp a ranar Lahadi 13 ga watan Agusta a makon farko a Ligue 1, inda ya ci kwallo daya a fafatawar.
Neymar wanda ya koma Faransa da taka-leda kan fam miliyan 200, ya kuma ci biyu a karawar da PSG ta doke Toulouse 6-2 a mako na biyu a gasar Faransa a ranar 20 ga watan Agusta.
Sauran kwallayen da Neymar ya ci sun hada da guda daya da ya zura wa Metz da wadda ya ci Celtic a gasar cin kofin Zakarun Turai ya kuma ci Bayern Munich daya duk a gasar ta Zakarun.
A ranar 30 ga watan Satumba ya ci Bordeaux biyu a fafatawar da PSG ta yi nasara da ci 6-2 a gasar cin kofin Faransa.
Daga nan ne Neymar ya ci Andelecht kwallaye biyu, daya a Paris daya a Belgium a gasar Zakarun Turai sannan ya zura wa Merseille daya a gasar Faransa.
Jumulla dan wasan ya ci kwallo 11 ya kuma taimaka aka ci tara, ya kuma karbi katin gargadi mai ruwan dorawa bakwai da jan kati daya da aka yi masa a karawa da Marseille.
Kwana dari da Neymar ya yi a PSG tana ta daya a kan teburin gasar Faransa, sannan ta kai zagaye na biyu a wasannin cin kofin Zakarun Turai.
Source: BBC Hausa
Title :
Neymar Yacika Kwana 100 A PSG
Description : A ranar 3 ga watan Agustan 2017 ne Neymar ya koma Paris St-Germain daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya. Dan wasan ...
Rating :
5