Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya ki amincewa ya sauka daga mulkin kasar yayin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba.
A jawabin da ya gabatar ga al'ummar kasar ta gidan talabijin ranar Lahadi, Mista Mugabe ya ce shi zai jagoranci babban taron jam'iyyarsa ta Zanu-PF wanda za a yi a watan gobe.
Sai dai tun da farko a ranar Lahadi ne Zanu-PF ta sauke shi daga shugabancin jam'iyyar.
Har ila yau jam'iyyar ta kuma kori matarsa Grace da kuma wadansu daga cikin manyan jam'iyyar.
Kuma jam'iyyar ta nada Mataimakinsa Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugabanta.
Karfin ikon Mista Mugabe ya fara raguwa ne a ranar Laraba, kan batun wanda zai gaje shi.
Rikicin ya samo asali makonni biyu da suka wuce bayan Mista Mugabe, mai shekara 93, ya kori Mista Mnangagwa daga aiki.
Abin da ya sa tsofaffin kwamandodin sojojin kasar suke ganin wani yunkuri ne na share wa matarsa hanyar maye gurbinsa.
Tun da farko, aranar Lahadi ne aka nada Mista Mnangagwa a matsayin sabon jagoran Zanu-PF kuma dan takarar jam'iyyar a babban zaben shekarar 2018.
Sai dai Mista Mugabe bai tabo wadannan batutuwan ba yayin da yake jawabi.
"Za a yi babban taron jam'iyya mai muki ta Zanu-PF a makonni masu zuwa kuma ni ne zan jagorance shi", in ji shi.
Mugabe ya ce yana sane da masu adawa da shi a cikin jam'iyyar Zanu-PF da rundunar sojin kasar da kuma al'ummar kasar, inda ya ce akwai bukatar dawo da Zimbabwe kan hanya.
A ranar Laraba ne sojojin kasar wadanda suke goyon bayan mataimakinsa suka yi wa Mista Mugabe daurin talala a birnin kasar Harare.
Masu zanga-zanga sun nufi fadar Shugaban Zimbabwe Shugaba Robert Mugabe don su bayyana bukatarsu ta shugaban ya sauka daga mulki a ranar Asabar.
Source: BBC Hausa
Title :
Mugabe Yaki Amincewa Ya Sauka A Kujeran Mulki
Description : Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya ki amincewa ya sauka daga mulkin kasar yayin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba. A jawabin da ya ...
Rating :
5