Shugaba Robert Mugabe ya bayyana a gaban al'umma a karon farko tun bayan da sojoji suka kwace ikon kasar a ranar Laraba da safe.
A ranar Juma'a ne aka ga Shugaba Mugabe na tafiya kan jar darduma sanye da kayan bikin kammala karatun digiri, inda ya shiga cikin taron daliban jami'a da ke bikin kammala karatu suna kuma rera taken kasar.
Wannan abu ne da dama Mista Mugabe ya saba yi duk shekara, sai dai ba a yi tsammanin zai yi hakan ba a bana, saboda yadda sojoji suke masa daurin talala tun ranar Laraba.
Har yanzu dai Janar-Janar din sojojin suna tattaunawa da Mista Mugabe kan yiwuwar ya yi murabus, don kawo karshen takun-sakar siyasar da ta yi kamari a kasar.
Da sanyin safiyar Juma'a ne rundunar sojin ta ce tana samun ci gaba wajen hakon masu laifi da suke zagaye da Mista Mugabe.
Wasu masu sa ido sun ce har yanzu Mugabe mai shekara 93, yana son ci gaba da mulkinsa.
Babban dalilin da ya sa har yanzu sojojin ke bin sa ta ruwan sanyi, shi ne ganin yadda za a iya samun sarkakiya da kuma tafiyar hawainiya a tattaunawar.
Source: BBC Hausa
Title :
Mugabe Ya Baiyana A Karon Farko Bayan An Kwace Mar Mulki
Description : Shugaba Robert Mugabe ya bayyana a gaban al'umma a karon farko tun bayan da sojoji suka kwace ikon kasar a ranar Laraba da safe. A rana...
Rating :
5