Kocin Manchester United, Jose Mourinho bai fayyace ko zai cika yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar ta shekara uku ba.
Kocin ya ce ya mayar da hankali wajen bunkasa United da kuma lashe kofin Premier da sauran gasar da suke buga wa kafin yarjejeniyar ta sa ta cika.
Mourinho dan kasar Portugal, ya kusan yin shekara daya da rabi a United, inda ya lashe League Cup da kofin Europa a bara, wanda hakan ya kai kungiyar gasar kofin Zakaraun Turai ta bana.
Mourinho mai shekara 54, ya shaidawa Daily Mirror cewa ya shiga yarjejeniyar shekara uku da United, ya kuma mai da hankali kan bunkasa kungiyar a fagen tamaula.
Ana rade-radin Mourinho zai koma Faransa kungiyar Paris-St Germain da horar da tamaula a nan gaba.
United tana ta biyu a kan teburin Premier bayan wasa 11 da ta yi, kuma wannan ne karon farko da kungiyar ta tagaza tun bayan da ta ci kofin Premier a 2012-13 a karkashin Sir Alex Ferguson.
Source: BBC Hausa
Title :
Mourinho Baida Tabbas A Manchester
Description : Kocin Manchester United, Jose Mourinho bai fayyace ko zai cika yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar ta shekara uku ba. Kocin ya ce ya mayar...
Rating :
5