Wani bincike ya nuna cewa maza sun fi kamuwa da bugun zuciya ta hanyar jima'i, fiye da mata.
Ko da yake, ba kasafai aka fi samun bugun zuciya ba a wajen jima'i.
Amma binciken ya ce 34 cikin 100 ne kadai daga cikin 4,557 aka tabbatar da sun kamu da bugun zuciya cikin sa'a daya a lokacin jima'i, kuma 32 daga cikinsu maza ne.
Sumeet Chugh, na wata cibiya da ke kula da lafiyar zuciya, ya ce bincikensa ne na farko da ya gano cewa jima'i na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da bugun zuciya.
Ya gabatar da binciken ne a wani babban taron likitocin zuciya da aka gudanar a Amurka.
Ana dai samun bugun zuciya ne idan zuciya ta daina bugawa. Matsalar kuma na iya sa mutum ya fita hayyacinsa, ya daina numfashi.
Dakta Chugh da wasu abokan aikinsa sun yi nazarin matsalolin zuciya ne da suka faru a kan mutanen da suka haura shekara 18 daga 2001 zuwa 2015 a Portland, Oregun.
Binciken ya ce ana samun matsalar a jima'i kasa da kashi daya, kuma wadanda matsalar ta fi shafa maza ne.
Source: BBC Hausa
Title :
Maza Sunfi Kamuwa Da Ciwo Zuciya Ta Hanyan Jima'i-Bincike
Description : Wani bincike ya nuna cewa maza sun fi kamuwa da bugun zuciya ta hanyar jima'i, fiye da mata. Ko da yake, ba kasafai aka fi samun bugun ...
Rating :
5