Kungiyar Marseille ta soke yarjejeniyarta da Patrice Evra yayin da kuma Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta dakatar da shi na tsawon wata bakwai bayan da ya harbi wani magoyin bayan kungiyarsu da kafa.
Evra, mai shekara 28, ya tokari dan kallon kwallon kafar ne da kafa a yayin da kungiyarsa ke shirin fafatawa da kungiyar Vitoria Guimaraes a farkon watan nan.
Yanzu an dakatar da Evra har zuwa watan Yunin 2018, tare da cin shi tarar yuro 10,000.
Dan wasan na Faransa na atisaye ne a lokacin da ya aikata laifin, matakin da ya sa aka ba shi jan kati tun kafin wasan.
Kuma Marseille ta yi rashin nasara da ci 1-0 a wasan.
Source: BBC Hausa
Title :
Marseille Ta Kori Patrice Evra
Description : Kungiyar Marseille ta soke yarjejeniyarta da Patrice Evra yayin da kuma Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta dakatar da shi na tsawon wata ba...
Rating :
5