Manchester United na shirin daukar Marco Asensio, za kuma ta ba shi yarjejeniyar shekara biyar a kungiyar, in ji wani rahoto daga Spaniya.
Kocin United, Jose Mourinho na neman 'yan wasan da za su kara masa karfin kungiyar a watan Janairu da wadanda za su buga masa tamaula a badi a Old Traford.
Jaridar Don Balon ta ce United za ta bai wa mai wasan tsakiya na Real Madrid fam miliyan 177 idan har ya amince zai koma buga gasar Premier.
Dan wasan mai shekara 21, yana da yarjejeniya da Real Madrid har zuwa kakar 2023, ya kuma ci kwallo hudu ya kuma taimaka aka zura biyu a raga a wasa takwas da aka fara da shi.
Sai dai kuma Isco na kokarin kwantar wa da Asensio hankali kan rade-radin da ake yi a kan dan kwallon.
Source: BBC Hausa
Title :
Manchester United Zata Dauki Marco Asensio Daga Madrid
Description : Manchester United na shirin daukar Marco Asensio, za kuma ta ba shi yarjejeniyar shekara biyar a kungiyar, in ji wani rahoto daga Spaniya. ...
Rating :
5