Tsohon dan wasan baya na Arsenal, Martin Keown, wanda ke cikin tawagar kungiyar da ta dauki kofin Premier a kakar 2003-04 ba tare da an doke ta ko sau daya ba ya ce manchester City ta kama hanyar kafa irin tarihin da suka yi na cin kofin ba tare da an doke su ba.
Keown wanda yake fashin baki kan wasan kwallon kafa a yanzu, wanya kasance cikin tawagar Arsenal da ta yi waccan bajintar, wadda aka yi wa lakabi da 'invincibles', ya ce yana ganin a yanayi da halin da Man City ke wasa a yanzu babu wata kungiya da za ta iya taka mata birki a gasar Premier.
Tsohon dan wasan ya ce yana fatan Man City ba za ta kawar da wannan tarihi da suka kafa ba, amma yadda yanayin yake a yanzu kusan ba makawa sai sun yi.
TALLA
Keown ya ce ba abin da zai dakatar da kociyan City, Pep Guardiola daga daukar kofin a bana, domin mutum ne da kusan ko da yaushe yake nasara.
Bayan tsohon dan wasan na Arsenal, shi ma Garth Crooks da ke yi wa BBC sharhi a kan wasan na tamola, yana daga cikin wadanda suka sallama wa Manchester City, bayan wasan da suka doke Leicester City 2-0, nasarar da ta kasance ta 16 a jere.
Rooks ya kara da cewa Man City bisa ga dukkan alamu ta kama hanyar kafa wani sabon tarihi a gasar Premier, domin ko a yanzu ma yadda kungiyar ke taka leda kusan yana daga cikin mafi kyau da aka taba gani a tarihin gasar.
Kungiyar ta Guardiola da ta kama hanyar daukar kofin na Premier ba kama hannun yaro, tana da maki 34 a wasa 12, abin da ya zo daidai da bajintar da suka yi a farkon kakar 2011-12, da suka dauki kofi, a lokacin kociyansu Roberto Mancini.
Source: BBC Hausa
Title :
Man City Tagama Cin Premier Bana-Keown
Description : Tsohon dan wasan baya na Arsenal, Martin Keown, wanda ke cikin tawagar kungiyar da ta dauki kofin Premier a kakar 2003-04 ba tare da an doke...
Rating :
5