Hukumomin Amurka sun amince a fara sayar da wata kwayar magani ta fasahar dijital karon farko a duniya.
Kamfanin Japan mai suna Otsuka ne ya samu izinin sayar da nau'in maganin da yake sarrafawa don masu larurar kwakwalwa da ake kira Abilify dauke da wani dan kankanin maballi a kowacce kwaya.
Da zarar an hadiyi kwayar maganin, sai ta aika sako zuwa wani abu da za a manna wa jikin maras lafiya wanda shi kuma zai rika tura bayanai zuwa wata manhaja a wayoyin zamani na marasa lafiya.
Fasahar daga nan tana iya raba wadannan bayanai tsakanin jami'an lafiya da kuma ma'aikatan kula da masu irin wadannan larurori.
Wannan Fasaha na da nufin kula da masu larurorin kwakwalwa kamar birkicewar tunani wadanda ba sa shan maganinsu ko yaushe, ko kuma sun manta su yi hakan.
Source: BBC Hausa
Title :
Magani Mai Fasahar Dijital Zai Shigo Kasuwa
Description : Hukumomin Amurka sun amince a fara sayar da wata kwayar magani ta fasahar dijital karon farko a duniya. Kamfanin Japan mai suna Otsuka ne y...
Rating :
5