Dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku ya kauce wa yuwuwar tura shi gidan maza a Amurka, bayan da ya amince ya biya tara ga 'yan sandan Beverly Hills, kan daukin da suka kai na damun makwabta da hayaniya daga gidansa.
Lukaku zai biya 'yan sandan kudin ne bayan da suka kai dauki kan kiransu da aka yi game da korafin hayaniya da makwabta suka yi daga wani gida da Lukakan yake haya a ciki a lokacin bazara.
An kama dan wasan mai shekara 24 a watan Yuli, sati daya kafin Manchester United ta saye shi daga Everton.
Dan wasan na Belgium zai biya dala 450, a matsayin diyya ko ramuwa ta amsa kiran da 'yan sandan suka yi kan korafin hayaniyar da ake yi a gidan nasa a lokacin.
Wannan na nufin an rage tuhumar, wadda a da ta kunshi babban hukunci na zaman gidan yari na wata shida.
A maimakon waccan tuhumar ta da yanzu ta zama ta damun jama'a, wadda ita kuma ta tanadi biyan tarar dala 100 da sauran wasu kudaden da kuma hukunci.
A ranar 18 ga watan Disamba, za a sake zaman sauraren shari'ar a kotun Los Angeles Airport Courthouse.
Source: BBC Hausa
Title :
Lukaku Ya Kauce Wa Zaman Gidan Yari A Amurka
Description : Dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku ya kauce wa yuwuwar tura shi gidan maza a Amurka, bayan da ya amince ya biya tara ga '...
Rating :
5