An dora dan wasan baya na kungiyar Mainz da kuma tawagar Najeriya Leon Balogun a karayar da ya yi a hannunsa na hagu, jinyar da za ta sa shi kaurace wa wasa tsawon makonni.
A ranar Juma'a ne ya ji raunin a lokacin atisaye a kungiyar tasa ta Jamus, abin da ya sa bai samu damar wasan da kungiyar ta yi a gida ba na Bundesliga, inda ta doke FC Cologne, ranar Asabar.
Kungiyar na fatan dan wasan zai warke kafin hutun gasar Jamus na huturu, wanda za a fara ranar 17 ga watan Disamba.
Kungiyarsa ta Mainz tana matsayi na 12 a teburin gasar Jamus da maki 15 bayan wasa 12. Bayer Munich ce ta daya da maki 29, sai Schalke04 da ke mara mata baya da maki 23, kamar yadda ta uku RB Leipzig ita ma take da maki 23, amma da bambancin kwallo daya tsakaninsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Leon Balogun Zai Yi Jinyar Makonni
Description : An dora dan wasan baya na kungiyar Mainz da kuma tawagar Najeriya Leon Balogun a karayar da ya yi a hannunsa na hagu, jinyar da za ta sa shi...
Rating :
5