An shawarci mata su dinga kwanciyar kaikaice a lokacin da cikinsu ya kai wata shida, domin hakan zai taimaka wajen hana haihuwar da ba rai.
Wani nazari da aka yi a kan mata sama da 1,000 dubu daya ya gano cewa akwai karuwa hadari ga mace ta dinga kwanciya a rigingine yayin da cikinta ya shiga wata shida.
Nazarin ya yi duba ne a kan mata masu ciki 291 da suka haifi 'ya'ya ba rai, da kuma mata 735 da suke haifar jariransu a raye.
Masu binciken sun ce yanayin kwanciyar da mata suke yi idan za su yi bacci shi ya fi matukar muhimmanci, kuma ka da su damu idan suka ga gansu a rigingine yayin da suka farka.
Kusan daya daga cikin mata masu ciki 225 a Birtaniya su kan haifi 'ya'ya ba rai, kuma nazarin ya kididdige cewa kusan jarirai 130 za a ceto a shekara idan mata masu ciki suna kwanciya da gefe daya.
Ko tashi daga bacci a rigingine na da matsala?
Farfesa Alexander Heazell, darakta ne a cibiyar Tommy da ke nazari kan haifar yara ba rai a asibitin St Mary da ke Manchester, wanda kuma shi ne ya jagoranci binciken, na bai wa mata masu ciki shawara a kan su dinga kwanciya da gefe daya idan za su kwanta, ko da kuwa da rana ne.
"Abin da ba a so shi ne mata masu ciki su farka a rigingine kuma su yi tsammanin wani abu mara kyau ka iya samun jaririnsu."
"Tambayar da muka yi ita ce, takamaimai wacce irin kwanciya mutane suke yi idan za su yi bacci, kuma shi ne abu mai muhimmanci idan mutum yana daukar lokaci mai tsawo a irin wannan kwanciyar fiye da yadda za ka yi a ko wanne bangare.
"Har ila yau kuma ba za ka iya yin wani abu game da yanayin da ka tashi ba, amma za ka iya yin wani abu game da yadda za ka kwanta bacci."
Abubuwan da ya kamata ka yi idan zaka yi bacci
Ki saka filo daya ko sama da haka a gefen bayanki don ya taimaka maki yin bacci ta gefe dayaIdan kuma kin tashi cikin dare, ki duba yanayin kwanciyar taki sannan ki koma baccinki ta daya gefenKi tabbatar da cewa a ko wanne lokaci za ki yi bacci to ki kwanta ta bangare maimakon rigingine, ko da rana ko da daddareIdan kin tashi a rigingine da daddare, kar ki damu kawai ki juya gefe daya ki ci gaba da baccinkiSai dai nazarin bai gano wani bambaci tsakanin kwanciya a gefen dama ko a hagu ba
Masu binciken ba za su iya cewa komai game da dalilin da ya sa ake samun karuwar haifar yara ba rai ba, sai dai akwai wasu bayanai da dama da aka tattara da suke nuna cewa a lokacin da mace mai ciki take kwanciya rigingine, nauyin jariri da na mahaifa na haduwa su takura jini inda hakan kuma kan haddasa wa jariri toshewar jinin da yake zagayawa da kuma iskar da yake samu.
Edward Morris na BJOG ya ce, "Mun yi matukar maraba da samun wannan sabon bincike".
"Wannan nazari ne mai matukar muhimmanci wanda zai kara tabbatarwa da jiki cewa yin bacci a ringine ga matan da cikinsu ya kai wata shida na sa su fuskanci barazanar haihuwar da ba rai," in ji shi.
Cibiyar nazari ta Tommy ta gabatar da wani gangami da zai kara wayar wa da mata kai a kan binciken da kuma ba su kwarin gwiwa wajen kwanciya da gefe daya.
Hakkin mallakar hotoFAMILY PHOTOImage captionMichelle Cottle mai shekara 36 tana zaune a Landan kuma ita ce wacce ta rubuta a a kan "Dear Orla"
Michelle Cottle ta haifi jaririnta Orla ba rai a mako na 37 a shekarar 2016, bayan da ta yi goyon cikinta lafiya ba tare da wata alama da take nuna cewa akwai matsala ba.
Ta yi wani rubutu a shafinta mai suna "Dear Orla" inda kuma ta ji ra'ayoyi daga wurin matan da suka shiga irin wannan yanayin.
Michelle ta sake haihuwar wata 'yar mai suna Esme bayan shekara daya, ta ce yana da muhimmanci iyaye su dinga aiki da irin wannan shawara da ake bayarwa don gujewa afkuwar abun da ba shi kenan ba.
"Ina ganin hakan zai taimakawa mutane, wajen gujewa abu mara kyau da ka iya faruwa, da kuma samun kyakkyawan yanayi fiye da na mutanen da suke samun matsala.
"Ko wanne lokaci ana iya samun wani yanayi da ba kasan ko jaririnka yana da rai ko babu ba, wannan wani abu ne na tashin hankali," in ji ta.
"Da daddare ne abun ya fi muni saboda mutane da dama suna iya cewa sun yi amanna cewar wata kila jariransu suna mutuwa ne a lokacin da suke bacci. Ina ganin wannan zai iya haifar da tsoro saboda yin bacci dai dole ne."
"Saboda haka ina ganin abubuwa a bayyane da za su iya taimaka maka abu ne mai mai matukar muhimmanci ga mata."
Source: BBC Hausa
Title :
Kwanciya Rigingine Ga Mata Mai Ciki Na Jawo Haihuwar Da Ba Rai
Description : An shawarci mata su dinga kwanciyar kaikaice a lokacin da cikinsu ya kai wata shida, domin hakan zai taimaka wajen hana haihuwar da ba rai. ...
Rating :
5