Abu daya zai sa ba za a taba mantawa ba da Mohammed Salah a tarihin kwallon kafa a Masar, saboda kwallo mafi muhimmaci da ya ci wa kasarsa a ragar Congo ana dab da a hure wasan da suka kara a watan Oktoba, wanda ya ba kasar nasarar shiga gasar cin kofin duniya karon farko bayan shekaru 27.
Sau bakwai Masar na lashe kofin Afrika amma tun 1990 rabon da kasar ta je gasar cin kofin duniya. Salah ne ya taimakawa kasar tsallakewa bayan ya ci fanareti a wasan da suka tashi ci 1-1 da Congo.
Cin kwallon ke da wuya murna ta barke da shagali a ciki da wajen filin wasan.
Duk da cewa Salah ya dade yana cin kwallaye, amma tarihi ba zai taba mantawa da shi ba a Masar, domin ya wadatar da 'yan kasar daga kishirwar da suka dade suna fama.
Salah ya samu yabo da girmamawa daga shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi.
Cin kwallon ne ya sa 'yan kasar ke yi wa Salah da kirari a matsayin "Sarkin Masar mai zamani" domin ko baya ga kwallon da ya ci a ragar Congo, Salah ya jefa kwallaye biyar a raga a wasannin bakwai da suka tsallakar da Masar zuwa Rasha.
Salah ya taka rawar gani a gasar cin kofin Afirka da aka gudanar a 2017, inda ya shiga sahun 'yan wasa 11 da aka zabo mafi shahara a gasar, bayan ya ci kwallaye biyu tare da taimakawa aka ci hudu.
Sannan ya taimakawa kasarsa zuwa matakin karshe a gasar, ko da yake Kamaru ce ta lashe kofin na Afrika.
Baya ga kasarsa, Salah sananne ne wajen cin kwallaye a kungiyoyin da ya ke taka leda musamman a Roma da Liverpool.
Tauraron Salah ya kara haskawa bayan ya dawo liverpool a watan Yuni, inda a watannin Agusta da Satumba aka bayyana shi a matsayin gwarzon dan wasan Liverpool.
Salah ya ci kwallaye 7 a wasannin Premier 11 da ya bugawa Liverpool, tare da cin kwallaye 5 a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai 6 da Liverpool ta buga.
A zamanin da yana Italiya, Salah ya taimaka wajen farfado da martabar Roma a Seria A, a kakar wasa daya da ya buga wa kungiyar inda ya ci kwallaye 15 tare d bayar wa aka ci kwallaye 11 a Lig . Kuma an kammala kakar 2016/2017 Roma na matsayi na 2 a teburin lig, tazarar maki hudu tsakaninta da Juventus.
Thierry Henry ya danganta Salah a matsayin dan wasa na musamman, amma ko dan wasan zai iya zama dan kasar Masar na farko da zai iya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na BBC bayan Mohamed Aboutrika da ya lashe kyautar a 2008.
Source: BBC Hausa
Title :
Kunsan Waye Muhammed Salah?
Description : Abu daya zai sa ba za a taba mantawa ba da Mohammed Salah a tarihin kwallon kafa a Masar, saboda kwallo mafi muhimmaci da ya ci wa kasarsa a...
Rating :
5