Ba a taba samun wani dan Afirka ba wanda ya fi kowa cin kwallaye a gasar Bundesliga har sai da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallaye 31 a kasar wasan 2016-17.
Wannan nasara ba wai kawai ta bai wa dan wasan dan asalin kasar Gabon damar dusashe tauraruwar dan wasan kasar Ghana, Tony Yeboah ba, wanda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye har karo biyu a 1990.
Pierre ne mutum na hudu a duniya da ya zarga kwallaye 30 a raga a gasar Bundesliga, irinsa na farko a tsawon shekara 40.
Wani kuma abun ban sha'awa dangane da nasarar fitaccen dan wasan na kungiyar Dortmund shi ne yadda ya ci kwallayen 31 a jerin wasanni 32, al'amarin da ya sanya kulob din nasa kasancewa na daya a gasar ta Bundesliga har karo biyu a jere sakamakon baiwar gudu da ta cin kwallaye da Allah ya huwace masa.
Kwallaye ukun da ya ci kulob din Benfica a wasa daya, a watan Maris ne suka sanya kididdigar jumullar kwallayen da dan wasan ya ci suka zama 40 a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Kwallon da ya ci a wasan da kulob dinsa ya ci Eintracht Frankfurt 2-1 wadda ta bai wa Dortmund damar daukar kofi a gasar wasan kwallon kafar Jamus na daya daga cikin kwallayen da ya ci 40.
Sakamakon kwazon Aubameyang mai shekara 28 ne ya sa aka sanya sunansa a jerin sunayen 'yan wasan da za a zabi gwarzon dan wasan duniya na FIFA.
Kuma Aubameyang ne dan wasa daya tilo daga Afirka a jerin 'yan wasan na FIFA, ko da yake Sadio Mane da suke takara tare domin lashe kyautar gwarzon Afrika na BBC yana cikin jerin 'yan wasan da ke takarar lashe kyautar Ballon d'Or.
Duk da tsammanin da ake da shi cewa dan wasan dan kasar Gabon wanda dan gayu ne zai bar kulob din Dortmund a karshen kaka har yanzu hakan bai kasance ba.
Manyan kungiyoyin wasa kamar Paris Saint-Germain da Manchester City sun nuna sha'awarsu kan dan wasan.
Sai dai kuma dan wasan ya dade yana burin buga wa kulob din da kakansa ya fi so wato Real Madrid, wasa, amma har yanzu burinsa bai cika ba sakamakon rashin nuna sha'awarsa, duk kuwa da irin baiwar cin kwallaye da ya nuna a Dortmund tun 2013.
Bugu da kari, a yanzu haka kwallayen da Aubameyang ya ci 135 a wasanni 204 na nufin zai iya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a kulob din Dortmund, kuma hakan na nufin zai iya zarta Michael Zorc daga nan zuwa karshen shekara.
'Auba' kara kwazo yake yi fiye da abun da ya yi a baya, a inda ya zura kwallaye takwas a wasanni shidan farko na gasar Champions League.
To sai dai idan an diba batun kimar kasar dan wasan ta asali wato Gabon a kwallon duniya, za a iya cewa kyaftin Aubameyang bai ji dadin yadda kasar tasa ta kasa kai bantanta a gasar zakarun kwallon kafar nahiyar Afirka ba duk kuwa da cewa shi ne mutumin da ya jefa kwallaye biyu a wasanni uku.
Abun tambaya a nan shi ne ko rawar da yake takawa a Dortmund za ta ba shi damar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka?
Source: BBC Hausa