Hukumar kwallon kafa ta Italiya ta sallami koci Giampiero Ventura, bayan da ya kasa kai ta gasar cin kofin duniya a karon farko da ta kasa zuwa tun 1958.
Italiya ta yi rashin nasara a hannun Sweden da ci daya mai ban haushi, sannan suka tashi babu ci a Milan, wanda hakan ya kawo karshen aikin Ventura mai shekara 69, wata 17 da ya ja ragamar Italiya.
Sai dai kuma Ventura ya ce tarihinsa da ya kafa a tawagar ta Italiya, daya ne daga cikin wanda ya fi fice tun bayan shekara 40.
Kocin ya ce wasa biyu kacal ya yi rashin nasara a kusan shekara biyu da ya ja ragamar Italiya a hirar da ya yi da 'yan jarida tun kafin hukumar ta sallame shi daga aikin.
Ventura ya maye gurbin Antonio Conte a watan Yunin 2016, ya kuma samu maki daya daga shida da ya kamata a karawa da ya yi da Spaniya da canjaras da Macedonia a wasan shiga gasar cin Kofin duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Kungiyar Kwallon Kafan Italiya Ta Kori Kocinta
Description : Hukumar kwallon kafa ta Italiya ta sallami koci Giampiero Ventura, bayan da ya kasa kai ta gasar cin kofin duniya a karon farko da ta kasa z...
Rating :
5