Wata babbar kotun Najeriya ta ce dakatarwar da majalisar dattawan kasar ta yi wa Sanata Ali Ndume ya saba wa doka.
Yayin zaman kotun a Abuja ranar Juma'a, Alkalin kotun, mai shari'a Babatunde Quadri, ya kuma ba da umarnin biyansa duka albashi da alawus-alawus din da ya kamata a biyasa na tsawon lokacin dakatarwar.
Har ila yau ya ba Sanata Ndume umarnin komawa bakin aikinsa a matsayinsa na dan majalisar dattawan kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) ya bayyana.
Sanata Ndume ya bayyana wa BBC ta waya cewa: "Alhamdulillahi godiya nake da Allah, kuma nasara ba tawa ba ce. Nasara ce ta dimokradiyya."
A ranar 30 watan Maris ne kwamitin da'a na Majalisar dattawan kasar ya dakatar da sanata Ndume bisa dalilin rashin cikakken bincike kafin gabatar da korafi a gabanta.
An dakatar da shi ne bayan kwamitin da'a na majalisar ya wanke shugabanta Bukola Saraki, da Sanata Dino Melaye daga zargin shigo da mota ba bisa ka'ida ba da kuma amfani da takardar shaidar digiri na bogi.
Source: BBC Hausa
Title :
Kotu Tabada Umarnin A Maida Sanata Ndume
Description : Wata babbar kotun Najeriya ta ce dakatarwar da majalisar dattawan kasar ta yi wa Sanata Ali Ndume ya saba wa doka. Yayin zaman kotun a Abuj...
Rating :
5