Bayan shekarun da ya yi wasa a matsayin aro, daga bisani ne ya koma Chelsea - inda ya zama daya daga cikin manyan 'yan wasa da suka taka muhimmiyar rawa wajen lashe kofin firimiya.
A ranar 1 ga watan Oktoba ne kocin Chelsea, Antonio Conte ya gwada sanya Moses a wasan da suka doke Arsenal da Liverpool, inda kocin ya gwada salon 3-4-3.
Wannan ne wasansa na farko a Chelsea a cikin fiye da shekara uku, amma Moses ya rika nuna kwazonsa da basirarsa.
Wasan da suka doke Hull City yana cikin wasanni 13 a jere da Chelsea ba ta sha kayi ba, kuma na 22 da Moses ya buga, sai dai daga bisani ya shiga jinyar raunin da ya ji a watan Afrilu.
A watan da ya gabata ne dan wasan ya kara sanya hannu a wani sabon kwantiragi da kolub din Chelsea, inda zai ci gaba da taka leda kungiyar, wadda ya fara koma a shekarar 2017.
Kalli bayani game da Victor Moses
Conte ya bukaci sabunta kwantiraginsa ne saboda yadda ya kara ganin kwarewar Moses a wannin share fagen fara kaka.
Dan wasan mai shekara 26, ya ce yana samun nasara ta hanyar nuna kwazo da natsuwa da kuma zafin nama.
Bayan lashe gasar firimiya, Moses yana cikin 'yan wasan Chelsea da suka zo na biyu a gasar Kofin FA, bayan Arsenal ta doke su, inda Moses ya samu jan kati.
Moses ya buga wa kasarsa wasa ne sau uku kadai a bana, amma a wasansa na farko ya ci kwallo a karawar da Najeriya ta doke Kamaru da ci 4-0, abin da ya sa Najeriya ta samu damar zuwa gasar Cin Kofin Duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Ko Kunsan Waye Victor Moses?
Description : Bayan shekarun da ya yi wasa a matsayin aro, daga bisani ne ya koma Chelsea - inda ya zama daya daga cikin manyan 'yan wasa da suka taka...
Rating :
5