Wani nazarin hotunan Ban-kasa da aka dauka da daddare sun nuna cewa hasken fitilun dan'adam na kara dallarewa kuma suna kara baibaye sararin duniya duk shekara.
Tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2016, hasken fitilun waje da mutane ke kunnawa na karuwa da fiye da kashi 2 cikin 100 duk shekara.
Masana kimiyya sun ce "asarar duhun dare" da ake samu a kasashe da dama na da illa ga "koshin lafiyar dan'adam da dabbobi da tsirrai.
Ayarin masu binciken sun wallafa sakamakon ne a cikin wata mujallar binciken kimiyya mai suna Science Advances.
Sun yi amfani da bayanai daga wata na'urar tauraron dan'adam ta Nasa - wadda takanas aka kera don auna walwalin hasken fitulun dare.
Inda suka gano cewa sauye-sauyen da ake samu ta fuskar karuwar haske tsawon lokaci ya sha bamban a tsakanin kasashe.
"Kasashen da suka fi haskakawa" a duniya, su ne Amurka da Spaniya, kuma su, ba su sauya ba.
Sai dai mafi yawan kasashe a Kudancin Amurka da Afirka da kuma Asiya na kara haskakewa.
Kasashe kalilan ne aka samu raguwar haskakawarsu, Yemen da Syria - dukkansu kuma na fuskantar yake-yake.
Hotunan dare daga tauraron dan'adama - na yankunan gabar teku da ke walwali da kuma tsare-tsaren yankunan birni masu sigar giza-gizai - na cike da kyawun gani, sai dai fitulun da dan'adam ke kunnawa suna da irin nasu illoli ga lafiyar mutane da ta muhalli.
Idan Rana ta fadi
A shekara ta 2016, Kungiyar Likitocin Amurka a hukumance ta gano "mummunan tasirin fitilar tsaro mai matukar haske da aka yi wa rarraunar kira", suka ce tana zuga mutane su "rage da kuma iyakance amfani da shudin kwan lantarki mai fitar da mafi karancin haske ta yadda za a rage dallare muhalli.
Sinadaran jikin dan'adam masu sa barci musammam sun fi tasiri a cikin shudin haske.
Wani nazari a baya-bayan nan da aka buga a mujallar Nature ya bayyana cewa hasken da mutane ke kunnawa na barazana ga barbarar furanni, don kuwa yana rage ire-iren wannan barbara da ake samu ta hanyar ƙwarin da ke karakainarsu cikin dare.
Bincike a Burtaniya ya bayyana cewa bishiyoyin da ke yankuna masu haske wal sukan feso furanni ne sama mako guda kafin wadanda suke wuraren da babu fitulun mutane.
Wani nazari da aka wallafa a farkon wannan shekara ya gano cewa sanya fitulu a birane ya haddasa "gawurtaccen sauyin" dabi'a ga tsuntsayen da ke kaura cikin dare.
Jagoran masu binciken, Christopher Kyba daga Cibiyar Binciken Kimiyyar bankasa ta Jamus da ke Potsdam ya ce bullo da hasken fitulun dan'adam na "daya daga cikin sauye-sauyen zahiri mafi kayatarwa da dan'adam ya kawo wa muhallanmu"
Ya ce shi da abokan aikinsa na sa ran ganin raguwar dallarewar haske a birane mawadata da shiyyoyin masana'antu a lokacin da suke komawa amfani da fararen kwayayen lantarki masu tsimin makamashi daga ja.
"Ina tsammanin cewa kasashe mawadata - kamar Amurka da Burtaniya da Jamus - za mu ga raguwar illahirin haske, musammam a yankunan da akan samu fitulu masu gau," ya ce wa BBC.
"Maimakon haka, sai muka ga kasashe kamar Amurka ta tsaya kamar yadda aka san ta a baya, amma Burtaniya da Jamus na kara samun haskakawar fitulu."
Tun da na'urorin tauraron dan'adam ba sa "ganin" hasken jan kwayaye da dan'adam ke iya gani, karuwar dallarewar hasken da muke samu zai ma fi abin da masu bincike suka auna.
Farfesa Kevin Gaston daga Jami'ar Exeter ya fada wa BBC cewa 'yan'adam na "kakaba wa kanmu wani zamani na hasken fitulu rakwacam".
'Ido ya fi gani, cikin haske kadan'
Farfesa Gaston ya ce "Haske, kawai abu ne da za kunna a inda ake bukatarsa amma ba a rika bata shi a inda ba a bukata ba."
Shi kuma Dr Kyba na cewa muna iya mayar da birane cikin yanayin dulum ba tare da mun janyo wata matsala ga magananmu ba.
"Ganin dan'adam ya dogara ne a kan yanayi mai sabani, amma ba yawan haske ba," ya yi bayani.
"Don haka ta hanyar rage sabanin yanayin a wajen gidajenmu - da kauce wa fitulu masu dallare ido - abu ne mai yiwuwa a samu gani mai inganci da haske kadan."
Source: BBC Hausa
Title :
Kasashe Dayawa Na Asaran Duhun Dare
Description : Wani nazarin hotunan Ban-kasa da aka dauka da daddare sun nuna cewa hasken fitilun dan'adam na kara dallarewa kuma suna kara baibaye sar...
Rating :
5