Masauki ne na kasaita da 'yan kasuwa da hanshakan attajiran duniya ke sauka, kuma duk wanda ya taba sauka ba zai taba mantawa da masaukin ba a matsayin daya daga cikin manyan otel da ake da su a duniya.
Ritz-Carlton, Otel ce da shugabannin kasashe da Firaministoci ke sauka, domin masauki ne na hamshakan attajirai.
Amma, kafofin yada labarai a Riyadh sun ruwaito cewa, otel din yanzu ya koma wani gidan yarin kasaita.
Kasa da watanni shida da shugaban Amurka Donald Trump ya sauka a Ritz-Carlton a ziyararsa ta farko a Saudiyya.
Sai ga shi yanzu masaukin na kasaita ya koma gidan yarin wasu shahararrun mutanen Saudiyya da suka saba sauka a otel din.
Wannan ya sa wasu ke danganta Otel din yanzu a matsayin wani "Babban gidan yarin kasaita a duniya".
An kame Yarimomi 'yan gidan sarautar Saudiyya da ministoci hudu da wasu manyan 'yan siyasa da suka hada da tsoffin ministoci, a wani mataki da gwamnatin kasar ta kira yaki da cin hanci da rashawa a Saudiya,
Cikin wadanda ake tsare da su har da Yarima Alwaleed bin Talal, hamshakin attajiri da ke da hannun jari a kamfanin Apple da Twitter.
Ko da yake, babu tabbaci daga hukumomin Saudiyya ko ana tsare su ne a cikin ginin otel din Ritz-Carlton, amma jaridar Guardian ta Birtaniya ta ambato wani babban jami'in gwamnatin kasar na cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ba zai kargame su ba a gidan yari.
Otel din wanda aka gina shekaru shida da suka gabata, yana da yawan daki 492, kuma girmansa da harabar ginin ya kai sukwaya mita 200,000.
Katifu a wani dakin kasaita
Wani bidiyo da jaridar New York Times ta wallafa a ranar Talata ya nuna katifu kanana da aka baza a wani babban dakin taro a Ritz-Carlton.
Bidiyon ya nuna wasu mutane a kwance, lullube da bargo a cikin otel din da kafofin yada labarai da dama suka ce wani dakin taro ne da ke daukar yawan jama'a kimanin 2,000.
Wata 'yar jaridar kafar talabijin ta Al Jazeera, Khadija Benguenna ta yada hotunan cikin ginin otel din, wasu mutanen kwance a katifu a shafinta na twitter.
Anuj Chopra wakilin kamfanin dillacin labaran AFP a Riyadh ya ruwaito cewa tun a ranar Lahadi 'Yan sanda ke sintiri a ciki da wajen ginin otel din, tare da rufe kofar shiga.
Sannan an wallafa wata sanarwa a shafin otel din na intanet cewa: " saboda wasu matsaloli da suka taso, an toshe shafin da tarho har zuwa wani lokaci".
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, bakin da suka riga suka kama daki a Ritz-Carlton a ranar Asabar an bukaci su kwashe kayansu inda aka canza ma su otel a birnin Riyadh.
Ko zan iya kama daki?
Shafin intanet na Ritz-Carlton ya nuna cewa babu daki da wani zai iya kamawa a watan Nuwamba, ko da yake, a tsakiyar Disamba an nuna mutum na iya kama daki biyu lokaci guda akan kudi 1,300 na riyals, kwatankacin dalar Amurka 350?
Source: BBC Hausa
Title :
Kasaitaccen Otel Yakoma Gidan Yarin Ministocin Saudiyya
Description : Masauki ne na kasaita da 'yan kasuwa da hanshakan attajiran duniya ke sauka, kuma duk wanda ya taba sauka ba zai taba mantawa da masauki...
Rating :
5