A ranar Juma'a ce wani kare da ya samu horon soji wanda kuma ya yi matukar taimakawa wajen ceton rayukan sojoji a Afghanistan zai karbi babbar lambar yabo wadda Birtaniya take bayarwa ga dabbar da ta yi namijin kokari a wani fada ko yaki.
Karen mai suna Mally, za a ba shi lambar yabon ne da aka yi wa lakabi da Dickin.
A shekarar 2012 ne aka yi wa Mally horo a kan yadda zai gano abubuwan fashewar da aka binne ko aka boye da kuma samun horo kan yadda zai iya gano abokan gaba.
Ya fara aiki da dakaru na musamman daga Birtaniya da Afghanistan domin fatattakar masu tayar da kayar baya na kungiyar Taliban daga wani gini a Kabul.
Sau biyu dai Mally na samun rauni bayan da ya shiga wuta a dalilin aiki inda ya je hutun jinya, bayan ya warke kuma ya dawo bakin aiki.
Source: BBC Hausa
Title :
Kare Zai Karbi Lambar Yabo A Afghanistan
Description : A ranar Juma'a ce wani kare da ya samu horon soji wanda kuma ya yi matukar taimakawa wajen ceton rayukan sojoji a Afghanistan zai karbi ...
Rating :
5