Shugaban mabiya Shi'a a kasar Ghana, Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin, ya bukaci hukumomin Najeriya da su saki Sheikh Ibrahim el-Zakzaky wanda ke tsare.
Ya bayyana hakan ne a birnin Accra lokacin da ya jagoranci tattakin Arbaeen , wato taron tuna wa da halin da jikan Manzon Allah (SAW), Imam Hussain, ya shiga a karni na bakwai.
Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin Najeriya take tsare da Zakzaky bayan wani rikici tsakanin mambobin kungiyarsa da sojoji a garin Zariya.
Shekih Abubakar ya ce: "Zakzaky kamar sauran malaman Shi'a ana gallaza masa kan zalunci. Idan za ka tambayi duniya mene ne Zakzaky ya yi, za a ce maka babu abin da ya yi".
Ya ce lokaci ya yi da ya kamata "gwamnatin Najeriya ta saki malamin don bai yi komai ba".
A makon jiya ne wata babbar kotu aNajeriya ta saki wadansu mabiya Shi'a 10da aka kama kuma aka gurfanar a gaban kuliya sakamakon rikicin da ya faru tsakaninsu da sojoji a watan Disamban shekarar 2015.
Kotun ta ce ta wanke su daga laifuffuka biyar da ake tuhumarsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Jagoran Shi'a Akasar Ghana Ya Bukaci A Saki Zakzaky
Description : Shugaban mabiya Shi'a a kasar Ghana, Sheikh Abubakar Ahmad Jamaluddin, ya bukaci hukumomin Najeriya da su saki Sheikh Ibrahim el-Zakzaky...
Rating :
5