Zlatan Ibrahimovic da Paul Pogba za su taka leda a wasan da Manchester United za ta kara da Newcastle ranar Asabar, bayan kammala doguwar jinyar raunin da suka ji.
Ibrahimovic, mai shekara 36, bai buga wasa koda daya ba a kakar bana saboda raunin da ya samu a gwiwa a watan Afrilu.
Pogba, mai shekara 24, shi ma ya fara jinya ne a watan Satumbar wanda kuma tun daga lokacin rabonsa da ya taka leda.
Hakazalika dan wasan bayan United, Marcos Rojo, zai buga wasan na ranar Asabar kuma kocin kungiyar Jose Mourinho ya ce "duka 'yan wasan uku ne zai yi amfani da su".
Rojo ya ji rauni ne a wasan da Ibrahimovic ya samu rauni wato a wasan kungiyar da Anderlecht a gasar Europa.
Source: BBC Hausa
Title :
Ibrahimovic Da Pogba Sun Dawo Taka Leda
Description : Zlatan Ibrahimovic da Paul Pogba za su taka leda a wasan da Manchester United za ta kara da Newcastle ranar Asabar, bayan kammala doguwar ji...
Rating :
5