A kalla mutum uku ne suka mutu bayan an yi hatsarin jirgin kasa a unguwar Agege da ke birnin Legas a kudancin Najeriya.
Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar jiragen kasa ta Najeriya da ke da hedikwata a Legas, Yakubu Mahmud, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar tirela da take kokarin tsayawa ta daki jirgin kasan.
Jirgin dai ya taso ne daga yankin Ijoko zai tafi yankin Ido da suke cikin birnin Lagos din.
Jami'in ya ce wadanda suka rasa rayukansu suna cikin wadanda suka fado daga bakin kofar jirgin.
Wasu rahotanni na cewa akwai yiwuwar yawan wadanda suka mutu ya karu domin akwai mutane da dama da suka ji munanan raunuka.
Ba a dai cika samun hatsarin jirgin kasa a Najeriya ba kamar su Indiya inda aka fi amfani da layin dogon.
Source: BBC Hausa
Title :
Hatsarin Jirgin Kasa Ya Kashe Mutane Da Dama A Lagos
Description : A kalla mutum uku ne suka mutu bayan an yi hatsarin jirgin kasa a unguwar Agege da ke birnin Legas a kudancin Najeriya. Shugaban sashen hul...
Rating :
5